NDLEA ta fadi jihar arewa da ta doke Kano a yawan masu safarar miyagun kwayoyi

NDLEA ta fadi jihar arewa da ta doke Kano a yawan masu safarar miyagun kwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana cewa jihar Kwara ce ta farko a sahun jihohin arewa da ake safarar miyagun kwayoyi.

Da take bayyana hakan a ranar Laraba, NDLEA ta ce jihar Kwara tafi ragowar jihohin arewa yawan gurbatattun mutane da ke safarar miyagun kwayoyi.

NDLEA ta gargadi jama'a da su guje wa safara da amfani da miyagun kwayoyi tare da yin kira ga jama'a da su kasance masu biyayya ga dokokin kasa.

Dandi Emmanuel, jami'in hukumar NDLEA, ne ya bayyna hakan a garin Ilorin yayin gabatar da jawabi ga manema labarai a matsayin wani bangare na aikin hukumar domin dakile safara da tu'ammali da miyagun kwayoyi.

DUBA WANNAN: Nadin mukamai: Aisha ta kara gwaba wa Buhari magana a fakaice

Ya gabatar da jawabin ne a wurin wani taro da hukumar tare da hadin gwuiwar kwamitin jihar Kwara mai yaki da shan miyagun kwayoyi.

A cewar Emmanuel, NDLEA ta kama mutane 91; mata 77 da maza 14, da laifukan safarar miyagun kwayoyi da suka hada da tabar wiwi da wasu kwayoyi daban-daban masu dumbin yawa a tsakanin watan Yuli na shekarar 2018 zuwa wannan shekara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel