Matan Najeriya 110 na mutuwa a kullum yayin haihuwa - UN
Majalisar dinkin duniya reshen kula da kidaya da kuma adadin mutane UNPF (United Nations Population Fund), ta ce a kalla kimanin Matan Najeriya 110 na mutuwa a kowace rana yayin haihuwa da matsalolin masu alaka da juna biyu.
Yayin taron karawa juna sani da kuma wayar da kai da aka gudanar a ranar Laraba 19, ga watan Yuni, shugabar reshen Madam Maryama Darboe, ita ce ta bayar da shaidar wannan bincike da kungiyar kula da lafiyar Mata masu juna da dauki nauyin gudanarwa.
Ta yi babatun yadda fiye da kaso 80 cikin 100 na Matan Najeriya ke ci gaba da dogaro tare da dabi'antuwa da haihuwa a gidajen su a madadin zuwa asibiti. Ta ce wannan lamari ya fi kamari musamman a tsakanin Matan Arewa.
Yayin da ya kasance kudirin majalisar dinkin duniya na tabbatar da ba a samu wata tangarda ba da ta za ta haifar da mutuwar ko da mace daya a yayin haihuwa, Madam Maryama ta hikaito yadda gwamnatin Najeriya ke kashe fiye da naira tiriliyan 1 cikin kowace shekara a fannin lafiya.
KARANTA KUMA: A gaggauta kawo karshen ta'addanci a jihar Taraba - Buhari ya gargadi hukumomin tsaro
Cikin na ta jawaban, jagorar kungiyar wayar da kai ta Najeriya, Hajiya Saudatu Sani, ta bayyana rashin jin dadi dangane da gazawar gwamnatin jihohin kasar nan a fannin kula da lafiyar Mata masu dauke da juna biyu.s
Domin muhimmiyar bukata a kan hakan, Hajiya Saudatu ta ce babu wani tanadin lafiya da za a yiwa Mata masu dauke da juna biyu da zai wuce gona da iri inda kuma ta nemi dukkanin masu ruwa da tsaki da su tabbatar da shimfidar tsare-tsare gami da fadakar da ma'aurata a kan alfanun tazarar haihuwa.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng