Dokar bayar da lasisin wa’azi: Kotu ta taka wa gwamnatin El-Rufai birki

Dokar bayar da lasisin wa’azi: Kotu ta taka wa gwamnatin El-Rufai birki

- Kotu ta haramta yunkuri da gwamnatin jihar Kaduna ke yi na bayar da lasisi ga masu wa’azi a karkashin dokar daidaita lamuran addini a jihar

- Kotun tace hana malaman addini wa’azi ba tare da lasisi ba ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya ba su ‘yancin yin Addini ba tare da tsangwama ba

- Sai dai kuma lauyoyin gwamnatin jihar ta Kaduna sun nuna aniyarsu ta daukaka kara zuwa gaba

Wata babbar kotu da ke Kaduna ta zartar da hukuncin cewa yunkuri da gwamnatin jihar karkashin mallam Nasir El-Rufai ke yi na bayar da lasisi ga masu wa’azi a karkashin dokar daidaita lamuran addini a jihar.

Fastocin cocin PFN ne suka shigar da kara kotu bisa zargin cewa hakan ya take yancinsu.

A cewar kotun, hana malaman addini wa’azi ba tare da lasisi ba haramun ne kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa gyara na shekarar 1999 wanda ya ba su ‘yancin yin Addini ba tare da tsangwama ba.

Alkalin kotun, Hon.Danladi Gwada ya kara da cewa, matakin da majalisar dokokin Kaduna ta dauka na ci gaba da aikin kafa dokar duk da cewa lamarin na gaban kotu da kuma umurnin da kotun ta bayar na dakatar da hakan, karan-tsaye ne ga kotun.

Kotun ta zartar da wannan hukunci ne a yau Laraba, 19 ga watan Yuni bayan cocin Pentacostal ya maka Gwamna El-Rufai, da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da kuma Babban Lauyan Jihar a gabanta game da dokar wa’azin a shekarar 2016.

KU KARANTA KUMA: Na karanta cewa baka bacci sosai, karanta wannan littafin – Shehu Sani ga Osinbajo

Sai dai kuma, a lokacin da ayarin lauyoyin wadanda ke kara suka bayyana gamsuwarsu da hukuncin kotun, lauyoyin gwamnatin jihar ta Kaduna sun nuna aniyarsu ta daukaka kara zuwa gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng