A karo na biyu, gwamnatin jihar Taraba ta kara saka dokar hana fita a Jalingo

A karo na biyu, gwamnatin jihar Taraba ta kara saka dokar hana fita a Jalingo

Darius Ishaku, gwamnan jihar Taraba, ya saka dokar hana fita daga gida a garin Jalingo biyo bayan barkewar sabon rikicin kabilanci a tsakanin al'ummar Kona da ATC.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bala Dan Abu, mai taimaka wa gwamna a bangaren sadarwa da yada labarai, ya fitar a daren ranar Litinin.

A cewar gwamnan, dokar hana fitar zata fara aiki daga karfe 4:00 na Asuba zuwa karfe 6:00 ba kowacce rana har sai sanarwa ta gaba.

Wannan shine karo na biyu da gwamnatin jihar Taraba ta saka dokar hana fita daga gidaje a garin Jalingo a cikin shekarar nan da muke ciki.

Gwamnatin jihar ta fara saka dokar hana fita a watan Maris biyo bayan barkewar rikici bayan an sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar.

Gwamna Isahak ya kara da cewa gwamnatin jihar ta umarci jami'an hukumomin tsaro da su tilasta jama'a yin biyayya ga dokar da aka kafa ta hana mutane fita daga gidajensu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar jama'a da dama a wasu sassan garin Jalingo sun kaurace wa gidajensu zuwa wasu unguwannin da ke garin. A cewar NAN, an samu musayar wuta da kone gidaje a tsakanin kabilun da ke rikici da juna.

Rikicin ya fi kazanta ne a tsakanin al'ummar da ke zaune a yankin Kona da ATC da ke gefen garin Jalingo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel