Takaitaccen tarihin tsohon Shugaban Masar Mohammed Morsi

Takaitaccen tarihin tsohon Shugaban Masar Mohammed Morsi

A yau Litinin, 17 ga Watan Yuni, 2019, ne Duniya ta samu labarin cikawar tsohon shugaban kasar Misra watau Mohammed Morsi. Shugaba Morsi ya yanke jiki ya rasu ne a na cikin shari’a da shi.

Mun kawo kadan daga cikin labarin rayuwar tsohon shugaban kasar Masar na farar hula da aka yi, wanda aka kifar da mulkinsa a 2013, aka kuma garkame a gidan yari bayan zargin shi da laifuffuka dabam-dabam.

1. Haihuwa

An haifi Ahmad Mohammed Morsi ne a cikin Watan Agustan 1951 a wani Kauye da ke Arewa da babban Birnin Cairo. Morsi ya na da ‘yan uwa maza 5 a gidan su. Marigayin ya yi karatu ne cikin hali da ba na jin dadi ba.

2. Malamin makaranta

Morsi ya karanta harkar kanikanci a jami’ar Cairo a cikin shekarun 1970s. Daga nan har ta kai ya samu Digiri na uku na PhD a wata jami’ar Amurka a 1985, bayan nan ya zama Farfesa jami’ar Zagazig ta Masar har 2010.

3. Shiga siyasa

Marigayi Morsi ya taba zama ‘dan majalisa mara jam’iyya a kasar Masar daga 2000 zuwa 2005 a lokacin da tsohon shugaban kasa Hosni Mubarak ya hana ‘yan kungiyar Ikhwan takara. Daga baya Morsi ya rasa wannan kujera.

KU KARANTA: Tsohon shugaba Mohammed Morsi ya rasu ana tsakiyar shari'a

4. Takarar shugaban kasa

A Ranar karshe na cike fam din shugaban kasa ne Morsi ya tabbatar da cewa zai yi takara a 2012, bayan ya hangi cewa za a iya dakatar da shugabansu Khairat Al-Shater daga takara. Haka kuma aka yi, ya samu mulki kamar wasa.

5. Lashe zaben 2012 da mulki

A tsakiyar 2012 ne Mohammad Morsi ya zama shugaban kasan Masar na 5 a tarihi. Morsi ya lashe 51.7% na kuri’un da aka kada a zagaye na biyu inda ya zama shugaban kasa na farko na farar hula bayan ya doke Ahmed Shafiq.

Morsi ya yi kokarin magance matsalolin kasar Masar kamar wahalar ruwa, cincirindo a kan hanyoyi, rashin tsaro da matsalar wutan lantarki da kuma wahalar man fetur. A cikin wannan hali aka hambarar da gwamnatinsa.

6. Dauri da hukuncin kisa

A cikin Watan Yunin 2013 ne zanga-zanga ya yi kamari inda gar ta kai Sojojin Masar a karkashin Abdel Fatah El-Sisi su ka hambarar da gwamnatin farar hula, su ka dare mulki. Daga nan aka daure Morsi aka yanke masa hukunci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel