Ka sayi wayar sata ka shekara bakwai a gidan yari - Hukumar yan sanda

Ka sayi wayar sata ka shekara bakwai a gidan yari - Hukumar yan sanda

-Hukumar yan sanda ta jihar Legas ta sanya wani mataki da zai sa a rage satar waya da wasu laifuffuka a jihar

-Hukumar ta ce duk wanda ya sayi wayar sata zai yi shekara bakwai a gidan yari ko sama da haka.

-Jami’in hulda da jama’a na hukumar DSP Bala Elkana ne ya bayyana haka, inda ya bayyana cewa hukumar na da hanyoyin da zata gano mutumen da ya siya wayar sata.

A kokarinta na ganin ta magance sata da wasu laifuffuka a jihar Legas, Hukumar yan sanda ta jihar ta sanar da wani hukunci mai tsanani akan duk wanda aka kama ya siya wayar sata.

A yau Asabar 1 ga watan Yuni, jami’in hulda da jama’a na hukumar ya gargadi mutane akan siyan wayar sata.

Elkana ya ce “A dokokin, mu ba karamin laifi bane mutum ya sayi wayar sata. Dokar tafi daurawa wanda ya siya wayar laifi fiye ma da wanda ya saci wayar. Hukuncin yafi tsanani akan wanda ya siya wayar fiye da barawon wayar.

“Dubarar yin wannan doka na da nasaba da magance matsalar sata saboda idan babu kasuwar da barayin zasu siyar da kayan satar to ba zasu saci wayar ba amma sabida suna da inda zasu siyar, shi yasa suke yin satar.

“Dalilin haka ne yasa dokar tayi hukunci mai tsanani akan wanda ya siya wayar fiye da wanda ya sace ta. Wanda yayi satar za a daureshi tsawon shekara uku amma wanda ya siya za a daure shi tsawon shekara bakwai kuma za a kwace kayan da satar idan muka gano shi.

“Don kada mutum ya siya kayan sata, to a shawarce ya siya kayan a kasuwa ba wai akan titi ba ko wajen mutanen da basu wannan harkar.

“Abu mafi mahimmaci shine idan muka kai wanda ya siya kayan satar kotu, zamu duba muga ko yana da masaniya cewa kayan sata ne. To ta yaya zamu gane hakan? Zamu duba muga nawa ake sayar da kayan a kasuwa, shi kuma nawa ya siya?

“Idan farashin abu a kasauwa Naira 100 ne, kai kuma ka siya Naira 10, to babu tantama cewa kasan kayan sata ne ka siya. Abu na biyu zamu duba muga a ina ka siya, shin a kasuwar da ake siyar da kayan ne koko ka siya ne a hannu wani a kan titi?

“Wannan ya ishi mutum yasan cewa kayan sata ne zai siya. Abu na uku, zamu duba lokacin da ka siya kayan. Wannan mahimman abubuwan ne zamu duba wajen gano ko mutum na da masaniyar cewa kayan sata ne zai siya.

“Idan ka lura zaka ga yanzu a bankuna, baya ga masu gadin bankin zaka ga akwai jami’an mu suna aiki tare da masu gadin bankin a cikin ginin bankin. Haka zalika muna yawan ganawa da shuwagabannin tsaro na bankuna don sake canza hanyoyin tsaron bankunan.”

KARANTA WANNAN: Zaben gwamnan Kaduna: Kotu ta sanya ranar da za’a cigaba da shari’a

Dan gane shiga na'ura da satar kudade ta yanar gizo, Elkana ya ce “Shiga na'urar mutane ta yanar gizo laifi ne na yanar gizo kuma zamu kama masu aikata hakan.”

Ana hakan ne Legit.ng ta ruwaito cewa Hukumar yan sanda zata kaddamar da manhajar waya wanda zai tayata magance matsalolin tsaro a fadin Najeriya.

A ranar Asabar 1 ga watan Mayu, hukumar yan sandan ta sanar a shafinta na tiwita cewa tana yin gwajin manhajar mai suna police –VSG.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: