Sabuwar Majalisar Buhari: Yaran Tinubu sun fara kulla kulla

Sabuwar Majalisar Buhari: Yaran Tinubu sun fara kulla kulla

-Yaran Tinibu sun fara kulla kullar hana Ambode zama minista a sabuwar majalissar Buhar

-Sunce zasu yi duk yadda zasuyi don ganin cewa ba a nada Ambode a matsayin minista ba, inda ma suke ikirarin cewa shi ba dan asalin jihar bane

-A martanin da ya mayar, wani tsohon hadimin Amboden yace a shirye tsohon gwamnan yake da duk abinda zasuyi

Akwai alamu cewa tsohon gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode zai zamo daya daga cikin sababbin yan majalissar Buhari.

Amma labaru na zuwa cewa mabiya bayan jigo a jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinibu sun fara kulla kullar hana a nada Ambode a matsayin minista.

Wani babban dan kungiyar Mandate, ya ce lokacin da Ambode yake gwamna ya ta'azzari yan jam'iyyar dayawa a Legas, a sabida haka, akwai bukatar a koya masa darasi.

Haka zalika, yan jam'iyyar sun fara shirye shiryen tuhumar tsohon gwamnan, Ambode ga hukumar EFFC a bisa zarginsa da satar kudin jihar.

Ambode ya dawo Najeriya yan kwana biyu da suka wuce daga kasar Faransa tun sadda ya bar kasar cikin watan Mayun wannan shekarar. Ana rade radin cewa yan majalissar Buhari na kusa kusa ne ke son Ambode.

Wata majiya a cikin jam'iyyar APC a legas ya zanta cewa Ambode bai da biyayya ga Jam'iyyar kuma ya batawa yan jam'iyyar dayawa, a sabida haka ba zasu amince a ayi mashi nadi ba.

Wata majiya daga jam'iyyar ya ce "Ambode yayi kokarin lalata mana jam'iyya. Baya ga cewa baya ganuwa, ya soke kwantiragin da aka baiwa wasu yan jam'iyya sa'annan ya kawo wasu kamfanoninshi. Ya kashe mamu dama ma su yawa a kokarinshi na ganin cewa ya durkussa da Sanwo Olu."

"Be yi mana kamfen ba sai de ya koma yana bin Buhari duk in da zaije. A sabida haka ba za mu amince a bashi kowane mukami ba don ya wakilci jihar Legas."

Wata majiyar ko cewa tayi "Ambode dan asalin jihar Ondo ne kuma koshi ba zai musanta haka ba. Eh yayi gwamna a jihar Legas saboda kundin tsarin mulki ya yadda da hakan. Amma kundin tsarin mulki cewa yayi dan asalin jiha ne kadai za a iya nadawa ya wakilci jihar a matsayin minista."

"Zamu tabbatar da cewa sanatocin mu uku sun hana a tan tan ce shi koda shugaban kasa Buhari ya tura sunanshi."

KARANTA WANNAN: Gwamna Ganduje ya nada sabon shugaban ma'aikata

Wata majiya ta kusa da Ambode ya ce tsohon gwamnan a shirye yake da duk abinda zasu yi. Ya kara da cewa shiru shirun gwamnan ba fa tsoro bane.

Tsohon hadimin Amboden ya ce "Ambode a shirye yake da duk abinda zasu yi tun da sun ci mutuncinshi. Buhari har rokonsu yayi da su bar Ambode ya sake komawa a matsayinsa na gwamna amma suka kiya. Sa'annan sukayi kokarin su tuge shi amma suka kasa."

"Su sani cewa Ambode ya rike mukamin babban sakatare a jihar sa'annan ya rike mukamin babban ma'aji na jihar kamin ya zama gwamna."

ya kara da cewa "Ya san sirrin duk masu kokarin bashi matsala. Duk wanda yake kokarin wulakantashi to fa yana gina ma kanshi ramin mugunta ne. Ba zance wani abu fiye da haka ba".

Anyi kokarin ayi magana da hadimin Tinubu amma hakan yaci tura kasancewar baya daukan kira sa'annan baya mayar da sakon waya.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: