An yi wa mahaifiyar Dangote da wasu matan Najeriya karramawa ta musamman

An yi wa mahaifiyar Dangote da wasu matan Najeriya karramawa ta musamman

Tsohuwar mai tace labarai, Hajiya Bilkisu Yusuf da mahaifiyar fitaccen dan kasuwa, Aliko Dangote, Hajiya Mariya Sanusi Dantata suna daga cikin mata 22 da aka saka sunayen su cikin jerin jaruman matan Najeriya da cibiyar cigaban mata ta Najeriya 'National Centre for Women Development' (NCWD) ta karrama.

Hajiya Bilkisu fittaciyar mai tace labarai a jaridu ce wadda ta rasu yayin aikin hajji na 2015 sakamakon cinkoso da aka samu a Saudiyya.

Hajiya Mariya yar kasuwa ce wadda ta yi fice wurin taimakawa al'umma. An zabe ta ne domin irin taimakon da ta ke yi wa talakawa. Tana ciyar da a kalla mutane 5000 a duk rana kuma tana bayar da gudunmawa ga cigaban mata da matasa.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 5 da ake gane takardan naira ta jabu

An kafa 'Nigerian Women Hall of Fame' ne domin tattara sunayen matan Najeriya da suka yi nasara a bangarorinsu daban-daban na rayuwa.

Uwar gidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari wadda ta samu wakilcin babban mai taimaka mata na musamman kan harkokin mulki, Hajia Hajo Sani ta shawarci matan da aka karrama su zama masu bayar da tarbiya ga kananan yara mata a kasar.

Sauran matan da aka karrama sun hada da marigayiya Alhaja Kudirat Abiola, Dakta Stella Ameyo Adadevoh, Alhaja Abibat Mogaji da Barista Oby Nwankwo.

Sauran sun ne; Mma Regina Achi Nentui, lyom Josephine Anenih, Senata Oluremi Tinubu (OON), Senata Binta Garba, Dakta Stella Okoli, Farfesa Adenike Osofisan, Mrs. Priscilla Ekwueme Eleje, Mrs. Adebimpe Bologun, Iyalode Alaba Lawson, Mrs. Folorunsho Alakija, Chief Nike Okundaye da Mo Abudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164