Yanzu-yanzu: Gwamna Bagudu ya sallami babbar alkaliyar jihar Kebbi kan tuhumar da tayi masa

Yanzu-yanzu: Gwamna Bagudu ya sallami babbar alkaliyar jihar Kebbi kan tuhumar da tayi masa

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya sallami mukaddashiyar shugabar alkalan jihar, Elizabeth Asabe Karatu, kan karar da ta shigar majalisar kolin shari'a cewa gwamnan ya ki tabbatar da ita saboda ba Musulma bace.

A wani biki na musamman da akayi ranar Juma'a a gidan gwamnatin jihar, gwamna Bagudu ya rantsar da Sulaiman Ambursa matsayin wanda zai maye gurbinta.

A makon nan, Asabe Karatu ta aika wasika majalisar kolin sharia NJC cewa ana take mata hakkin tabbatar da ita saboda Kirista ce.

A wasikar, Asabr Karatu ta laburta cewa siyasar addini da son gaskiyarta yace gwamnan ke take mata hakki duk da cewa NJC ta bayar da goyon bayan tabbatar da ita.

Hakazalika ta yi gargadin cewa NJC tayi iyakan kokarinta wajen ganin cewa ba'a nada Sulaiman Ambursa ba saboda ta'amuni da rashawarsa.

A ranar 17 ga Junairun 2019, majalisar dokokin jihar Kebbi ta tabbatar Asabe Karatu matsayin tabbatacciyar shugabar alkalan jihar, amma gwamnan ya ki amincewa.

KU KARANTA: Wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani dangane da matar shugaban kasa Aisha Buhari

Alkali Esther na gab na yin ritaya daga aiki, sakamakon zata cika sharuddan yin ritaya daga Alkalanci a ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2019, wanda hakan ke alanta da gangan gwamnan ke jan kafa kan bukatar Esther har sai ta yi murabus.

Sai dai sakataren gwamnatin jahar Kebbi, Babale Yauri ya musanta zargin Esther, inda yace babu yadda za’ayi gwamnan ya tabbatar da ita a matsayin Alkalin Alkalai bayan majalisa bata tantanceta ba, yace majalisar hakan ya faru ne saboda akwai rudani a cikin takardun karatunta.

Don haka yace wasikar da aka ce majalisar ta aika ma gwamna inda take shawartarsa ya tabbatar da Esther a matsayin Alkalin Alkalai ba gaskiya bane, wasikar bogi ce saboda babu sa hannun kowa akanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel