Wasu malaman jami'a a dakin otal suka samu kwalinsu na doctora - Tsohon Shugaban jami'a

Wasu malaman jami'a a dakin otal suka samu kwalinsu na doctora - Tsohon Shugaban jami'a

-Shugaban ASUU farfesa Abiodun Ogunyeni ya ce an samu lalacewar al'amurra a jami'oin Najeriya

-Haka zalika Farfesa Ikenna Onyido ya ce mafi yawancin jami'on Najeriya basu kai yadda ake tunanin sun kai ba

-Onyindo yayi ikirarin cewa wasu malaman jami'oin a dakin otal suka samu Phd dinsu.

Farfesa Ogunyemi, shugaban kungiyar ASUU kuma tsohon farfesa a jami'ar Nnamdi Azikiwe(Unizik), Awka, a jihar Anambra da farfesa Onyido sunce wasu jami'oin Najeriya basu kai yadda ake kuranta su ba.

Malaman biyu sun yi jawabi ne a wajen kaddamar da wani littafi na farfesa Ikenna Onyido a jami'ar Unizik, inda suke cewa ilimi ya gurbace ba kamar yacce yake a shekarun 60s da 70s ba.

A lokacin da yake jawabinsa, farfesa Oyindo ya ce karatun jami'a ya lalace inda ya kai ga yanzu wasu farfesoshin basu iya yin aikin koyarwa.

Onyido tsohon mataimakin shugaban jami'ar aikin gona ta Umudike da ke jihar Abia ya ce mafi yawancin jami'oin Najeria ana kuranta su ne.

"Najeriya ce kadai kasar da kowa zai iya koyawa a jami'a. Kamata yayi ace jami'a waje ne na tataccen ilimi inda ma'iya da masana kadai ke aiki. Kamin kazama mai koyarwa dole ka zama mai kwarewa" a cewarshi.

A cewar shi "a kwai malaman jami'ar da suka samu takardar karatunsu na uku a dakin otal" amma suna koyawa a jami'a.

"Muna yaye daliban da basu da isasshen ilimi kuma suna samun manyan yan siyasa su basu aikinyi a matsayin malaman jami'a. Ya kamata musan abinda muke bukata matsayin jami'oi"

KARANTA WANNAN: Wata kungiya ta bukaci a binciki Obasanjo da Jonathan

Haka zalika a lokacin da yake magana da yan jarida, farfesa Ogunyemi ya ce ana samun lalacewar ilimi ne saboda shuwagabannin siyasa basu damu da harkar ilimi ba. Ya ce tun dawowar dimukaradiyya ba a sake maida hankali ga harkar ilimi ba.

"Saboda bamu ba harkar ilimi mahimmacin da ya kamata shi ya sanya muke samun kowanne irin mutane a harkar ilimi. Bama tabbatar da dokoki da ka'idojin ilimin jami'oi saboda yan siyasa basu damu da hakan ba"

Tun farko Legit.ng ta ruwaito cewa kungiyar ASUU bata da masaniya cewa gwamnatin tarayya ta amince da Naira biliya 25 don a abiya malaman jami'a kudin alawus alawus dinsu.

A lokacin da yake zantawa da yan jarida a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu 2019 Prof. Ogunyemi ya bayyana cewa basu da masaniya dangane da maganar da ministan ilimi Adamu Adamu yayi game da kudin da aka amince abiya.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwer: http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng