Sadiq Kurba ya zama kakakin majalisar Gombe

Sadiq Kurba ya zama kakakin majalisar Gombe

- An rantsar da Abubakar Sadiq a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Gombe na shida

- An zabi Shuaibu Haruna Adamu daga Gombe ta arewa a matsayin mataimakinsa

- A sabon majalisar dokokin, APC ce mafi rinjaye inda take da mambobi 19 yayinda PDP ke da mambobi biyar

An zabi wani mamba mai wakiltan Yamaltu ta yamma a majalisar dokokin jihar Gombe, Abubakar Sadiq Ibrahim, a matsayin kakakin majalisar jihar na shida a ranar Juma’a, 14 ga watan Yuni.

Ibrahim wanda aka fi sani da Sadiq Kurba, ya kasance mamban majalisar a karo na biyu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A tuna cewa tuni Gombe ta arewa ta samar da Gwamna Muhammed Inuwa Yahaya, yayinda mataimakinsa, Dr Manasseh Daniel Jatau ya fito daga Gombe ta kudu.

Haka zalika, an zabi Shuaibu Haruna Adamu mai wakiltan Kwami ta gabas daga Gombe ta Arewa a matsayin mataimakin kakakin majalisa.

KU KARANTA KUMA: An shiga rudani yayinda tsawa ta sauka a ofishin yan sanda a Wukari, Taraba

Daga Ibrahim har Adamu sun dauki rantsuwar aiki karkashin jagorncin magatakardar majalisar jihar, Alhaji Shehu Muhammad Atiku, kasancewar su kadai aka tsayar a matsayin.

An tattaro cewa APC ce mafi rinjaye inda take da mambobi 19 yayinda PDP ke da mambobi biyar.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Manasah Daniel Jatau, mataimakin gwamnan jihar Gombe, ya bukaci sauran mataimakan gwamna da su mutunta gwamnonin jiharsu maimakon yin gasa wajen bayar da umurni domin samun alaka mai kyau da cima manufa guda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel