Shegiyar uwa: Wata mai jego ta gudu ta bar jaririyarta a asibiti

Shegiyar uwa: Wata mai jego ta gudu ta bar jaririyarta a asibiti

Wata mata da har yanzu ana nemanta ta gudu ta bar sabuwar jaririyarta a asibiti bayan haihuwa a asibtin mata dake Osumeyi, karamar hukumar Nnewi dake jihar Anambara, kudu maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa matar ta shiga asibitin ne yayinda ta fara nakuda kuma likitoci suka karbeta.

Jaridar The Nation ta samu labarin cewa yan mintuna kadan bayan samun nasarar haihuwa, matar ta arce daga asibitin zuwa inda babu wanda ya sani har yanzu.

Tabbatar da wannan labari, kakakin hukumar yan sanda, Haruna Mohammed, ya ce an kammala shirye-shiryen mika jaririyar ga gidan marayun gwamnati domin raino da kula.

KU KARANTA: Atiku da PDP sun roki kotu wata alfarma guda daya

Yace: "A ranar Litinin, 10/06/2019 misalin karfe 11:20 na safe, an kawo wata mata mai juna biyu asibitin tana nakuda."

"Da wuri aka tarbeta kuma cikin mintuna goma sha biyar ta samu nasarar haihuwar diya mace. Sai ma'aikatan suka koma kula da wasu mara lafiyan."

"Bayan haihuwa, sai matar ta bace daga asibitin ta bar diyarta a baya. Jami'an yan sanda sun kai ziyara asibitin kuma sun yi kokarin nemo matar domin hukunta ta."

A labari mai kama da haka, ciki ya dori ruwa yayinda aka nemi sabuwar jaririya aka rasa a asibitin jihar Plateau. Daga baya aka gano cewa wani likitan bogi ne ya yi awon gaba da jaririyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel