Mummunar arangama ya yi sanadin mutuwar Sojoji 10 da yan Boko Haram 64 a tafkin Chadi

Mummunar arangama ya yi sanadin mutuwar Sojoji 10 da yan Boko Haram 64 a tafkin Chadi

Rundunar dakarun hadaka ta kasashen dake makwabtaka da Najeriya, MNJTF, ta bayyana cewa ta yi asarar zaratan Sojojinta guda goma a wani kazamin karanbatta da suka yi da yan kungiyar ta’addanci ta Boko Harama a Arewacin Kamaru.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kaakakin rundunar MNJTF, kanal Timothy Antigha ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni, inda yace anyi wannan gumurzu ne a garin Darak dake Arewacin kasar Kamaru kusa da yankin tafkin Chadi.

KU KARANTA: Allah Ya tona asirin Limamin da ya shirya damfarar mabiyansa N3,000,000

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito kanal Antigha yana cewa kamar yadda rundunar tayi asarar Sojojinta guda 10, itama ta kashe mayakan kungiyar Boko Haram guda dai-dai har 64, sa’annan ta tafka ma kungiyar barna mai tsanani.

Antigha yace kimanin mayakan Boko Haram 300 dukkaninsu dauke da muggan makamai ne suka kaddamar da hari a Darak a cikin makonnan, amma zaratan Sojojin rundunar basu yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da biki, a haka aka kwashe tsawon sa’o’I ana fafatawa.

A sanadiyyar wannan turnuku, an kashe fararen hula guda takwas, an jikkata Sojoji guda takwas haka zalika Sojoji sun cafke yan ta’adda guda takwas, yayin da suka kwace dimbin alburusai da samfurin makamai daban daban.

Daga karshe Antigha yace wannan jarumta da sadaukarwa da dakarun MNJTF suka nuna ya yi daidai da manufar rundunar na fatattakar yan Boko Haram daga yankin tafkin Chadi, tare da tabbatar da tsaro a yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel