Yaki da Boko Haram: Gwamnan jahar Adamawa ya dira tsakiyar dajin Sambisa

Yaki da Boko Haram: Gwamnan jahar Adamawa ya dira tsakiyar dajin Sambisa

A wani ziyara na ba zata, sabon gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri tare da sauran shuwagabannin hukumomin tsaro dake jahar sun kutsa kai har cikin dajin Sambisa da yan Boko Haram suka mayar dashi gidansu.

Gwamnan ya shiga dajin kamar yadda jaridar Fombina Times ta bayyana a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, kuma hakan na cikin matakan da yake shirin dauka domin samar da ingantaccen tsaro a jahar Adamawa.

KU KARANTA: Za mu cigaba kamar yadda China da India suka cigaba – Shugaba Buhari

Yaki da Boko Haram: Gwamnan jahar Adamawa ya dira tsakiyar dajin Sambisa

Fintiri
Source: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya bayyana damuwarsa da ayyukan wata kungiyar matasa bata gari da ake kira da suna ‘Shila Boys’, wanda bayanai suka tabbatar da sun mayar da wani sashi na dajin Sambisa mafakarsu.

Dajin Sambisa na tsakanin tafkin Benuwe ne a wajen garin Jimeta, kuma yayi kaurin suna wajen bayar da mafaka ga nau’o’in miyagun mutane daban daban da suke shiga garin Yola su tafka ta’asa, sa’annan su koma dajin.

A jawabinsa, gwamnan jahar ya dauki alwashin kawo karshen duk wani nau’in matsalar tsaro a jahar Adamawa domin samar da zaman lafiya da cigaba mai daurewa a jahar, musamman duba da yadda yan shila suka fitini jama’a da fyade, sata, fashi da kuma kashe mutane ba tare da wani laifi ba.

Umaru Fintiri wanda ya taba zama gwamnan rikon kwarya a jahar Adamawa ya sake zama gwamna a karo na biyu ne bayan ya lallasa gwamna mai ci, Bindow Jibrilla a zaben gwamnoni n shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel