Za mu fitar da sunayen masu neman tayar da fitina a kasa ta hanyar kafafen sada zumunta - DSS

Za mu fitar da sunayen masu neman tayar da fitina a kasa ta hanyar kafafen sada zumunta - DSS

- Hukumar 'Yan sandan Farar Hula (DSS) ta ce ta kama wasu 'yan Najeriya da ke amfani da shafin sada zumuntarsu wurin yada kalaman da ka iya tayar da rikici a kasa

- Kakakin DSS, Afunanya ya ce matakin da suka dauka ya zama dole saboda wasu marasa kishin kasa suna wallafa bayyanai da za su iya kawo rikici a kasa

- Afunanya ya bayar da tabbacin cewa hukumar za ta cigaba da kamawa da hukunta masu aikata irin wannan rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta

Hukumar 'Yan sandan Farar Hula (DSS) ta gargadi 'yan suyi takatsantsan da irin abubuwan da suke wallafawa a shafukansu na sada zumunta saboda ta fara farautar mutanen da ke wallafa abubuwan da ka iya janyo rikici a kasa.

Premium Times ta ruwaito cewa 'yan sanda farar hulan ta fara kama wasu 'yan Najeriya da aka samu suna wallafa rubuce-rubuce masu hadari a shafukansu na sada zumunta.

DUBA WANNAN: Mutane 7 da su kayi bakin jini saboda gwagwarmayar 'June 12'

A sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, kakakin Hukumar DSS, Peter Afunanya ya ce nan ba da dadewa ba za a fitar da sunayen wadanda aka kama da wannan laifin.

A cewarsa, hakan ya zama dole ne saboda wasu marasa kishin kasa suna amfani da kafar sada zumunta wurin "wallafa rubuce-rubuce wurin yin kalamai marasa amfani ko saka tsoro da firgici a zukutan mutane."

Ya kara da cewa, "An gano hakan ne ta hanyar rubuce-rubucen karya da suke wallafa a intanet wanda aka yi domin jefa kiyaya tsakanin kungiyoyi daban-daban na kasar.

"Su kan canja gaskiya yadda abubuwa suka faru domin cimma wata manufar su ta janyo rikici tsakanin kabilu a kasar. Kawo yanzu an kama wasu masu aikata wannan laifin."

'Yan sanda sirrin sun kara da cewa, "za su tabbatar da cewa masu son jefa gaba tsakanin kabilu da masu shirya makirci ta hanyar siyasa ko kabilanci ba su cigaba da samun damar yin hakan ba a shafukan sada zumunta domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar."

DSS ta ce za ta cigaba da bibiyar masu aikata irin wannan laifin tare da 'kama su da gabatar da su gaban kuliya don fuskantar hukunci.'

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel