'Yar shekara 17 ta debi piya-piya don an saki mahaifiyarta a Kano

'Yar shekara 17 ta debi piya-piya don an saki mahaifiyarta a Kano

Wata yar jihar Kano, mai shekaru 17 da haihuwa, Sadiya Shehu, mazauniyar Tudun Murtala, karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano ta kashe kanta a ranar Litinin sakamakon rashin jituwan da ya auku tsakanin iyayenta har ya kai ga sakin mahaifiyarta.

Ta kashe kanta ta hanyar shan maganan kwari wanda akafi sani da piya-piyan da kke dakin mahaifiyar.

Yayinda manema labarai suka isa gidan marigayiyar, masu ta'aziyya sun cika gidan inda owa ke mika nashi sakon jajen.

Mahaifin yarinyar ya zanta da Chronicle, Malam Shehu Lawan ya tabbatar da cewa Sadiya ta kashe kanta ne kan wani dan kankanin abun da ya faru tsakaninsa da mahaifiyarta a ranar Lahadi kuma sun sulunta kansu a ranar.

KU KARANTA: Da duminsa: An damke masu garkuwa da mutane 3 da muggan makamai

Yace: "Na samu matsala da mahaifyarta kuma ta nuna bacin ranta. Tana kuka kuma na fada mata komai ya wuce. Na waye gari da safe na bar Sadiya da yan uwanta cikin koshin lafiya amma yayinda nake wajen aiki, na samu kiran cewa an kai ta asibiti."

Likitoci sun yi iyakan kokarinsu wajen ceto rayuwarta amma haka Allah ya kaddara, ta mutu "

Yayinda aka tambayesa shin ana shirin yiwa Sadiya aure ne, mahaifin ya tabbatar da cewa lallai ani ya zo neman aurenta kuma an bukacesa ya turo iyayensa. Ya yi alkawarin turosu idan mahaifinsa ya dawo daga kasar Saudiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel