Pogba ya bayyana Kante a matsayin dan wasan da yafi bashi matsala

Pogba ya bayyana Kante a matsayin dan wasan da yafi bashi matsala

-Paul Pogba ya bayyana dan kasarsu N’golo Kante a matsayin abokin hamayya mafi wahalar tunkara

-Dan tsakiya kwallan fa na kungiyar Manchester United ya hadu da kante a kakar wasanni uku kenan

-Duka yan wasa biyun sun yiwa Faransa kwallan a zo a gani a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a shekarar da ta wuce

Dan wasan kungiyar kwallan kafa Paul Pogba ya bayyana dan wasan kwallan kungiyar Chelsea N’golo Kante a matsayin abokin hamayya mafi wuyar tunkara a tarihinsa na kwallon kafa.

Yan wasa biyun sun taimaki kasar Faransa inda suka kaita ga cin kofin gasar kwallan duniya da aka gudanar a Rasha cikin 2018.

Amma tshon dan kwallan kungiyar Juventus din, wanda yanzu yake buga gasar Firimiya ya tunkari dan kasar tasu tsawan kakar wasanni uku kenan, inda ya bayyana shi a matsayin abokin hamayya da yafi takura masa.

Babu shakka dan wasan na kasar Faransan ya hadu da manyan abokan hammayya ciki ko hadda yan kwallo mafi iyawa a duniya kamar Messi da Ronaldo.

A wata hira da ya gudanar da jaridar The times, an bukaci dan wasa mai shekara 26, da ya bayyana dan wasan da yafi bashi wahalar tunkara a tarihinsa na kwallo

Abinda ya ba mutane da yawa mamaki shine yadda Pogba ya tsamo dan kasarsu N’golo Kante a matsayin wanda yafi bashi wahalar tunkara.

KARANTA WANNAN: KEDCO ta kaddamar da tiranfomomi 170 da motocin aiki 60

Kante de ya tabbatar da wajensa a cikin jerin yan wasan da ake take kowane wasa dasu a kungiyar ta Chelsea.

Tun farko, Legit.ng ta ruwaito cewa kungiyar Juventus na a kagare su kawo Pogba cikin kungiyarsu don inganta tsakiyar kungiyar.

Jaridar Mirror ta ruwaito a 2018 cewa Pogba na a fama da matsaloli a zamansa cikin kungiyar Manchester United tun zuwanshi a shekarar 2016.

Daga bisani, ana tsammanin Pogba na shirin ficewa daga kungiyar ta Firimiya bayan da aka siyoshi kan kudi Euro miliyan 89 shekaru uku da suka wace.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng