Burina shine hada kan Najeriya- jawabin Buhari a ranar damokradiyya

Burina shine hada kan Najeriya- jawabin Buhari a ranar damokradiyya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa a wajen taron bikin ranar Damokradiyya wanda ke gudana a Abuja a yau Laraba, 12 ga watan Yuni.

Buhari ya bayyana cewa babban burinsa a matsayinsa na Shugaban kasar Najeriya shine ya gay a hada kan kasar.

Shugaban kasar ya kuma yi tsokaci akan lamarin tsaro wanda ke ci ma kasar kwarya a tuwa inda ya bayyana cewa lamarin baya tsorata su illa ma kara masu kwarin gwiwa da hakan ke yi.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci aikin duk wanda ke so ya tsokani ko yi wa al'adun kasar ba'a ba ko kuma ya kawo wa tsaron kasa cikas.

Ga cikakken jawabin Shugaban kasar:

"Bambancin 2015 da 2019 dangane da harkar tsaro shi ne cewa a wannan karo muna yin aiki tare da jam'ian tsaro masu yawa da bayanan sirri da kuma kayan aiki.

"Ba mu tsorata da kalubalen da ke gabanmu ba sai dai ma sun kara mana kwarin gwiwa ne.

"Shirye-shiryenmu na habbaka rayuwar 'yan kasa (N-power da ciyar da 'yan makaranta) abin koyi ga sauran kasashen duniya.

"A matsayina na shugaban komitin farfado da tafkin Chadi zan jagoranci zama na musamman don kawo karshen matsalolin tsaro a yankin.

KU KARANTA KUMA: Bai isa ace ka kaddamar da 12 ga watan Yuni ranar Damokradiyya ba – Atiku ya caccaki Buhari kan rashin mutunta doka

"Ina mika godiya ta musamman ga 'yan kasuwa wadanda suka gina wuraren kasuwanci kamar layukan wayar hannu da kuma sauran wurare wadanda suka bai wa matasanmu aikin yi.

"Wannan gwamnati ba za ta yadda da aikin duk wanda yake so ya tsokani ko yi wa al'adunmu ba'a ba ko kuma ya kawo wa tsaron kasa cikas.

"Daga yau na mayar da sunan babban filin wasa na kasa da ke Abuja Moshood Abiola.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel