Wani matashi dan shekara 29 ya halaka kansa a jihar Kebbi

Wani matashi dan shekara 29 ya halaka kansa a jihar Kebbi

Wani matashin dalibi dan shekara 29 na Waziri Umaru Federal Polytecnic , Birnin kebbi kuma mazauni a unguwar badariya, wanda aka bayyana a matsayin Solomon Benedict ya halaka kansa a dalilin matsanancin talauci.

Benedict dai ya halaka kansa ne ta hanyar shan maganin kwari a cikin madarar yogut. Abokananshi sunyi kokarin ceto rayuwarshi amma abin yaci tura.

A lokacin da yake zantawa da yan jarida ranar Talata, 11 Yuni 2019, wani aboki marigayin ya bayyana cewa “ mun lura da cewa bashi da sauran sukuni. Ya kama cikinsa sai daga baya muka lura cewa ya gauraya maganin kwari cikin abin shansa. Ya rasa ransa kafin mu ceto shi."

Bayanai sun nuna cewa matashin ya rasa ransa a lokacin da ake kokarin kaishi asibiti mafi kusa don ceto rayuwarshi.

Karanta wanna: Jawabin da Jam'iyyar PDP ta yi bayan nada sababbin shugabannin Majalisa

Wata abokiyar mamacin dake a garin Jega, ta zanta da yan jarida inda kuma ta bukaci a sakaye sunanta ta ce” tun da dadewa yake ce mani zai kashe kansa, idan matsanancin talaucin da yake fama dashi bai rage ba. Amma ban taba yadda da gaske yake ba.

Na tuna duk sanda ya ziyarce ni a Jega, yana zanta mani akan matsin da yake fama dashi na rashin kudi, sai in bashi yan kudin mota da zai koma Birnin kebbi, kuma yakan gaya mani cewa idan lamarinshi bai inganta ba zai kashe kanshi."

Ta kara da cewa "Nayi mamaki matuka lokacin da na samu kiran waya daga Sokoto ana fada mani cewa Solomon ya kashe kansa

Mai magana da yawun Hukumar yan sanda ta jihar Kebbi DSP Nafi’u Abubakar, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga yan jarida a lokacin da yake zantawa dasu ta waya a ranar Talata, 11 Yuni 2019.

Yace ”kwarai muna da masaniya akan afkuwar lamarin. Yaron shekararshi 29. Ya halaka kansa a unguwar badariya dake Birnin Kebbi"

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe: http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: