Dabara: Yadda aka yiwa wata mata wayo kafin a gudu da jariri mai watanni 20 a duniya

Dabara: Yadda aka yiwa wata mata wayo kafin a gudu da jariri mai watanni 20 a duniya

Wani abun takaici ya faru a bangaren yara na Cocin 'SS John and Paul Iba Pope' dake unguwar Awada a garin Onitsa a jihar Anambra.

Wata mata, da ya zuwa yanzu ba a san ko wacece ba, ta yi awon gaba da jaririn mai suna Chibueze da misalin karfe 9 na safiyar ranar Lahadi bayan ta yiwa mai rainon jaririn wayo.

Muguwar matar ta bawa mai rainon Chibueze kudi tare da umartar da da ta je ta saka a cikin daron ajiye sadaka dake cikin zauren Cocin.

Matar ta karbi Chibueze daga hannun mai rainon domin ta je ta ajiye sadakar ta dawo, amma bayan ta jefa sadakar ta dawo sai ta nemi matar da Chibueze ta rasa.

Chibueze na da shekara daya da watanni 8 ne kacal a duniya.

DUBA WANNAN: Abinda yasa na gudu na bar gidan miji na - Matar tsohon gwamnan PDP

Tun bayan sace Chibueze ba a tuntubi iyayensa ba balle a yi zargin cewar ko masu garkuwa da mutane ne suka yi dabara wajen sace shi.

Ana yawan samun matsalar sace mutane tare da yin garkuwa da su har sai an biya kudin fansa a sassan Najeriya.

Yawaitar matsalar ne ya saka babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa, Muhammad Abubakar Adamu, ya kafa wata rundunar atisaye ta musamman da ya rada wa suna 'Puff Adder' domin magance miyagun aiyuka, musamman garkuwa da mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel