Siyasar Kano: Majalisar dokokin jahar Kano ta yi zaben sabon kaakakin majalisa

Siyasar Kano: Majalisar dokokin jahar Kano ta yi zaben sabon kaakakin majalisa

Dadadden dan majalisa dake wakiltar mazabar Ajingi a majalisar dokokin jahar Kano, Honorabul Abdul Aziz Garba Gafasa ya zama sabon kaakakin majalisar dokokin jahar Kano a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito jim kadan bayan samun amincewar takwarorinsa yan majalisa aka rantsar da Garba Gafasa a matsayin sabon kaakakin majalisar dokokin jahar Kano ta 9, tare da Honorabul Hamisu Chidari a matsayin mataimakin kaakaki.

KU KARANTA: Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka manyan kwamandojin Boko Haram 9

Siyasar Kano: Majalisar dokokin jahar Kano ta yi zaben sabon kaakakin majalisa
GAFASA
Asali: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gafasa ya dade a majalisar ta Kano, inda har ya taba zama kaakakin majalisa a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011 zamanin wa’adin mulkin Gwamna Malam Ibrahim Shekarau na biyu.

A shekarar 1962 aka haifi Abdul Aziz Garba a kauyen Gafasa dake cikin karamar hukumar Ajingi, inda yayi karatun Firamari a makarantar Toranke daga shekarar 1969 – 1976, sai karatun sakandari a kwalejin Birnin Kudu daga 1976 – 1981, inda yayi karatun difloma a makarantar cigaban karkara daga 1981 – 1983, daga karshe ya samu babbar difloma daga kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna.

Majalisar dokokin ta Kano tana dauke da yayan jam’iyyar APC guda 23, yayin da jam’iyyar adawa ta PDP keda yan majalisu 13, haka zalika Gafasa ya samun goyon bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tun a wani taron masu ruwa da tsaki daya gudana a fadar gwamnatin jahar a daren Asabar.

A wannan zama, Ganduje ya nuna rashin amincewarsa da dan takarar kaakakin majalisa mai barin gado, Alhassan Rurum wanda ya nuna yana goyon bayan Salisu Doguwa a matsayin wanda zai gajeshi.

Sauran yan majalisun da suka samu goyon bayan Ganduje a matakin mukamai daban daban sun hada da Labaran Madari a matsayin shugaban masu rinjaye, Kabiru Dashi bulaliyar majalisa da Hayatu Daurawar sallau mataimakin shugaban masu rinjaye.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel