Matan Ghana sun fi na Najeriya iya soyayya da rikon amana - In ji wani Saurayi

Matan Ghana sun fi na Najeriya iya soyayya da rikon amana - In ji wani Saurayi

- Wani dan Najeriya mazaunin Ghana ya bayyana cewa matan Ghana sun fi Najeriya iya soyayya

- Ya ce babu abinda matan Najeriya suka iya idan ba su yaudareka su cinye maka kudi su gudu ba

Wani saurayi dan Najeriya wanda ya shafe shekara takwas yana zaune a kasar Ghana, mai suna Moses Balogun, ya auri wata 'yar Ghana, sannan ya bayyana cewa iya soyayya ce tasa ya aureta maimakon ya auri 'yar Najeriya.

A wata hira da yayi da BBC, Moses ya bayyana cewa matan Ghana sun fi na Najeriya iya soyayya da rike amana.

Balogun ya bayyana cewa, ya taba yin soyayya da 'yar Najeriya abin bai kare musu da dadi ba, saboda a karshe ta yaudare shi ne.

Matan Ghana sun fi na Najeriya iya soyayya da rikon amana - In ji wani Saurayi

Matan Ghana sun fi na Najeriya iya soyayya da rikon amana - In ji wani Saurayi
Source: Facebook

Ga yadda hirar ta su ta kasance da wani jami'in BBC:

Zaka iya yi mana bayanin tarihin rayuwarka a takaice?

Sunana Moses Balogun, ni dan Legas ne a Najeriya, ni kuku ne a Zen Garden a nan kasar Ghana. Shekarata takwas a Ghana, kuma ina auren 'yar Ghana.

Tsakanin matan Najeriya dana Ghana wadanne suka fi iya soyayya?

Gaskiya zan zabi 'yar Ghana ne, ina son halayensu, idan suna soyayya da kai suna sonka da zuciya daya ne. Amma matan Najeriya ba haka abin yake ba, saboda na taba yin soyayya da wata sai ta yaudareni daga karshe.

KU KARANTA: Kwadayi mabudin wahala: Wani saurayi yayi kuskuren turawa budurwarsa N250,000 a lokacin da yake kokarin yi mata kyautar N25,000

Tsakanin Najeriya da Ghana, ina zaka zaba a matsayin kasa?

Ina son wannan tambayar, tana da kyau, gaskiya Ghana ta fi, ba zan yiwa kowa karya ba. Saboda har yanzu akwai cin hanci sosai a Najeriya. A Ghana kuwa akwai 'yanci da adalci. Idan ka zo Ghana idon ka zai bude sosai. Ka da ka bari wasu su gaya maka abin da zaka gani, ka zo da kanka ka ganewa idonka zaka yarda da abinda nake fada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel