Kwadayi mabudin wahala: Wani saurayi yayi kuskuren turawa budurwarsa N250,000 a lokacin da yake kokarin yi mata kyautar N25,000

Kwadayi mabudin wahala: Wani saurayi yayi kuskuren turawa budurwarsa N250,000 a lokacin da yake kokarin yi mata kyautar N25,000

- Wani saurayi yayi kuskuren turawa budurwarsa makudan kudade a lokacin da yake kokarin yi mata kyautar N25,000

- Budurwar ta rufe duk wata hanya da saurayin zai tuntube ta bayan taga shigowar kudin cikin asusunta

Wani saurayi dan Najeriya ya gamu da wani iftila'i yayin da tsautsayi ya sanya ya tura mata naira dubu dari biyu da hamsin a lokacin da yake kokarin tura mata naira dubu ashirin da biyar, a cikin asusun bankin ta.

Saurayin yana so ya yiwa budurwar tasa kyautar naira dubu ashirin da biyar, tsautsayi ya sanya yaje ya saka sifili guda hudu maimakon guda uku, inda kudin ya zama naira 250,000.

Kwadayi mabudin wahala: Wani saurayi yayi kuskuren turawa budurwarsa N250,000 a lokacin da yake kokarin yi mata kyautar N25,000

Kwadayi mabudin wahala: Wani saurayi yayi kuskuren turawa budurwarsa N250,000 a lokacin da yake kokarin yi mata kyautar N25,000
Source: Facebook

Ya kirata domin ya nuna mata cewa kuskure yayi, amma yarinyar da a lokacin take ganin kamar ta samu tsuntsu daga sama gasasshe taki tsayawa ta saurare shi.

A karshe ma yarinyar tayi rufe duk wata hanya da zai iya kiranta ko ya tura mata sako, inda ta shiga cikin jihar Legas take ta bushashar ta da kudin.

Mutumin yayi kokarin ya sanar da jami'an tsaro akan lamarin.

KU KARANTA: 'Yan arewa na da damar fitowa takarar shugaban kasa a 2023 - Shittu

Ga dai abinda mutumin ya rubuta a kasa:

"Ina so na kai rahoton wannan lamari zuwa ga 'yan sanda da hukumar EFCC. Ina da adireshin shagon mahaifiyarta. Nayi kuskuren tura mata 250,000 a lokacin dana ke kokarin tura mata 25,000. Ta zo ta kwana a gurina ranar Laraba. Ta kirani tayi mini godiya bayan na tura mata kudin, na yi kokarin nayi mata bayanin cewa kuskurene, sai ta kashe wayar kuma ta rufe duk wata hanya da zan iya tuntubar ta. Kuma na ganta jiya tana ta daukar hoto a Eko Atlantic ita da abokanta.

Ita ce macen da nake tunanin na samu a matsayin matar aure. Bana son rikicin shafukan sada zumunta, amma ina so na sanar da ita cewa ina so ta dawo mini da kudina ko kuma taga rashin mutunci irin wanda bata taba gani ba," in ji saurayin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel