Komai yayi farko zai yi karshe: An ba Sanatoci kwana 3 su mika makulan ofishinsu

Komai yayi farko zai yi karshe: An ba Sanatoci kwana 3 su mika makulan ofishinsu

Hukumar majalisar dokoki ta ba mambobin majalisar dattawa masu barin gado kwanaki uku don su mika makullan ofishinsu.

Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ne ya ba da sanarwar a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni, a farkon taron bankwana na majalisar dokoki na takwas a zauren majalisar Abuja.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rahoto cewa sanarwar ya kasance ajanda na hudu a takardar ranar.

Majalisar dattawan ta takwas wacce aka rantsar a ranar 9 ga watan Yuni, za ta zo karshe a ranar 6 ga watan Yuni.

Saraki ya bukaci yan majalisar da su mika makulan a tsakanin Alhamis da Asabar.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa bayan ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni, Sanata Danjuma Goje ya janye daga tseren takarar kujerar Shugaban majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Tambuwal yayi sabbin nadi masu muhimmanci a gwamnatinsa

A yanzu dai Goje ya jadadda goyon bayansa ga Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan domin darewa kujerar.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ne ya bayyana hakan bayan ganawr sirri da suka yi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel