Neman lafiya: Mazauna Abuja sun koma ga bokaye da masu maganin gargajiya

Neman lafiya: Mazauna Abuja sun koma ga bokaye da masu maganin gargajiya

Rahotanni sun kawo cewa mazauna wasu garuruwan birnin tarayya, Abuja, sun bayyana cewa sun gwammaci zuwa wajen Bokaye domin neman warakar cuttutuka da ke kama yaransu maimakon garzayawa asibiti.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa hujjarsu akan haka shine cewar babu asibitoci a kusa dasu.

Wata mai maganin gargajiya da aka ambata da suna Fatima Yusuf ta ce ta dade tana duba yara sannan tana ba iyaye magani domin warkar da ‘ya’yan su idan suka kamu da ciwo.

Fatima tace tana samo magungunanta ne a can cikin kungurmin daji. kuma a duk lokacin da ta ba yaro sai kaga ya samu sauki ya warke.

Haka shima wani dattijo mai suna Musa Sarki, ya bayyana cewa shine kusan babban likiti a wannan gari nasu.

Ya bayyana cewa yara na warkewa sannan kuma iyaye na jin dadin maganin mu. Shi dai magungunan baya wuce idan mun hada sai aje gida a dafa a baiwa yaro.

KU KARANTA KUMA: Guru Maharaji ya bukaci Buhari ya nada shi a matsayin mai bashi shawara domin ya jagoranci ma’aikatar man fetur da sauransu

A wani labbari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Jami’an tsaro na Civil Defence a Borno a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, sun tabbatar da kama wani Aliyu Muhammed, mai shekaru 24 wanda ake zargin shi kaiwa yan ta’addan Boko Haram kayayyakin hada bama-bamai a Maiduguri.

Kwamandan rundunar, Ibrahim Abdullahi ya bayyana hakan a hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Maiduguri.

Abdullahi ya bayyana cewa jami’an rundunar sun kama mai laifin ne a ranar 25 ga watan Afrilu, biyo bayan wani rahoton kwararru da suka samu yayinda yake a hanyarsa ta kai wa yan ta’addan Boko Haram kayayyakin bam.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel