Buhari bai amince da samar da 'yan sandan jiha ba - Fadar Shugaban kasa

Buhari bai amince da samar da 'yan sandan jiha ba - Fadar Shugaban kasa

Sabanin rahotanni da suka bayyana a baya, fadar shugaban tayi karin haske na bayar da tabbacin matsayar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan samar da 'yan sandan jiha a fadin kasar nan ta Najeriya.

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce batun amincewar shugaban kasa Buhari wajen bayar da lamunin samar da 'yan sandan jiha a fadin kasar nan kanzon kurege ne da bai inganta ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta musanta rahotanni da suka bayyana amincewar shugaban kasa Buhari na samar da 'yan sandan jiha. Sai dai babu shakka shugaban kasar ya amince da korar wasu jami’an yan sanda 37 da aka kama da miyagun laifuka.

Kamar yadda kwamitin mutum uku da shugaban kasa ya kafa domin gudanar da bincike akan reshen hukumar 'yan sanda na SARS, shugaban kasa Buhari ya bayar da lamunin sa na sauya sunan reshen zuwa ARS, Anti Robbery Squad.

Wannan jawabi ya zo ne a ranar Litinin da sanadin babban hadimi na musamman ga shugaban kasa Buhari akan hulda da al'umma da kuma kafofin sadarwa, Mallam Garba Shehu.

KARANTA KUMA: Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin dakaru a jihar Borno

Bayan karbar sakamakon bincike da kwamitin ya gudanar a kan samar da 'yan sandan jiha a fadin kasar nan, shugaba Buhari ya bukaci tsawon watanni uku domin zurfafa tunani da kuma gudanar da dogon nazari na yiwuwar hakan a kasar nan.

Kazalika shugaban kasa Buhari ya bayar da lamunin sa akan shawarar umartar sufeto janar na 'yan sanda wajen bankado wasu 'yan sanda 22 da aka cafke dumu dumu wajen aikata laifuka na cin zarafin dan Adam.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel