Masu tsattsaurar ra'ayi a Denmark sun kone Kur'ani kurmus don Musulmi sun shirya bude baki a kasarsu

Masu tsattsaurar ra'ayi a Denmark sun kone Kur'ani kurmus don Musulmi sun shirya bude baki a kasarsu

Rahotanni da muke samu sun nuna cewa masu tattsaurar ra’ayi sun gudanar da zanga-zanga hadi da kona Alkur’ani kurmus domin nuna adawa da gagarumin bude bakin da aka shirya a Copenhagen babban birnin kasar Denmark.

Masu zanga-zangar baya ga kone Kur'ani mai tsarki sun kuma kasance dauke da allunan dake rubuce da "Turai Tamu ce".

Kungiyoyin jin kai ne suka shirya gagarumin bude baki a guraren shakatawar gwamnati dake birnin Copenhagen.

A ko wace shekara dai masu tsatsaurar ra'ayi kan gudanar da tarzoma domin kalubalanatar taron bude baki da ake shiryawa a kasar.

Shugaban Stram Course ta masu tsattsaurar ra'ayi, Rasmus Paludan da mambobin jamiyyunsa sun halarci filin shakatawar gwamnati a lokacin bude baki inda suka gudanar da zanga-zanag tare da kone Kur'ani mai girma.

'Yan sanda sun bayyyana a gurin jin kadan bayan bayyanarsu suka kuma kori masu tsattsaurar ra'ayin daga yankin.

KU KARANTA KUMA: Mazan Kirista su auri mata sama da guda daya, babu ayar Injila da ya haramta hakan - Fasto

A dayan bangaren kuma kungiyar zaman lafiya a kasar sanye da riguna masu ruwan dorawa sun goyi bayan Musulmi inda suka kalubalanci masu tsatsaurar ra'ayi. Sun kuma jira a fagen bude bakin har sai da aka kammala lamun lafiya.

Masu tsattsurar ra'ayi sun bayyyana jin kadan bayan kiran sallar Magariba gaban wani otel dauke da allunan da aka rubuta "Turai Tamu ce" suna kuma rike da lasafikan da suka dinga rera taken kalubalantar Musulmi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel