Hukumar NDLEA ta yi babban kamu a jihohin Anambra da Kaduna

Hukumar NDLEA ta yi babban kamu a jihohin Anambra da Kaduna

-Wani mai fataucin miyagun kwayoyi ya shiga hannun hukumar NDLEA a jihar Anambra, inda aka kama shi dauke da garin koken da kuma tabar wiwi.

-A jihar Kaduna kuwa hukumar har wa yau ta samu irin wannan nasara inda ta damke kwayoyin taramol guda 950,000 wanda aka kiyasta kudinsu ya kai N45m.

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato NDLEA reshen jihar Anambra ta yi nasarar cafke Chimezie Okoye wani hasabibin mai fataucin miyagun kwayoyi a Awka babban birnin jihar.

Kakakin hukumar mai suna Charles Odigie Efosa shi ne ya bada wannan sanarwa. Efosa ya ce, Okoye wanda aka fi sani da Don ya shigo hannu ne a shiyyar Ifite Awka.

Hukumar NDLEA ta yi babban kamu a jihohin Anambra da Kaduna

Hukumar NDLEA ta yi babban kamu a jihohin Anambra da Kaduna
Source: UGC

KU KARANTA:Bikin 12 ga watan Yuni ya fi daraja fiye da na 29 ga watan Mayu – Buhari

Ya ce, an kama wannan mutum a ranar 25 ga watan Mayu dauke da garin koken da kuma kilo 3.3 na tabar wiwi a gidansa dake Awka.

Ya kara da cewa, nan bada jimawa ba za’a tura shi zuwa kotu domin a zartar masa da hukunci.

A wani labari makamancin wannan kuwa, hukumar NDLEA reshen jihar Kaduna ta cafke kwayar Taramol a kasuwar Sheikh Gumi dake Kaduna. Kwayar dai an kiyasta cewa kudinta ya kai N45m.

Kwamandan hukumar a jihar Kaduna, Bala Fagge yace kwayar ta Taramol wace ta kai adadin 950,000 an shigo da ita garin ne daga Onishan jihar Anambra.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel