An rantsar da sabon gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, amma an fita dashi saboda rashin lafiya

An rantsar da sabon gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, amma an fita dashi saboda rashin lafiya

Ana cikin bikin rantsar da sabon gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, aka fitar da shi daga farfajiyar taron saboda rashin lafiya da yake fama da shi.

Wannan abu ya faru ne a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu bayan rantsar da sabon gwamnan da mataimkainsa, Umar Kadafur.

Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa sabon gwamna, Umara Zulum, bai kai ga kammala jawabinsa na farko a matsayin gwamna ba kafin aka fitar da shi daga farfajiyar saboda gaza magana.

An rantsar da sabon gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, amma an fita dashi saboda rashin lafiya

sabon gwamnan jihar Borno Babagana Zulum
Source: Facebook

Kamfanin dillanci Najeriya ta bada rahoton cewa babban alkalin jihar Borno, Kashim Zanna, ya rantsar da sabon gwamnan ne a taron da dubunnan mutan jihar Borno, shugabanni da manyan jami'an gwamnati suka halarta.

Tsohon gwamnan, Kashim Shettima, ya bayyana farin cikinsa kan mika ragamar mulki ga wanda yake kyautatawa zaton mutumin arziki ne kuma kwararre wanda zai iya kawo cigaba ga jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel