An tsaurara matakan tsaro a Gombe yayinda aka rantsar da Inuwa Yahaya a matsayin gwamna

An tsaurara matakan tsaro a Gombe yayinda aka rantsar da Inuwa Yahaya a matsayin gwamna

An baza jami’an tsaro a ciki da wajen babban filin wasan Pantami a Gombe a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, yayin da ake gudanar da bikin rantsar da Inuwa Yahaya a matsayin zababben gwamnan karo na hudu a mulkin damukardiyya a jihar Gombe.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa jami’an tsaro suna ta faturol a manyan titunan zuwa babban filin wasan Pantami da birnin Gombe.

Hukumomin tsaro a jihar, hade da rundunar yan sanda, rundunar Civil Defense da na DSS duk sun yadu a wurare daban-daban a harabar filin wasan.

Jami’an hukumar kare afkuwar hatsarurruka sun tantance al’umma masu yawa wadanda suka hallaro don shaida bikin rantsarwan tare da kula da zirga-zirga.

An tsaurara matakan tsaro a Gombe yayinda aka rantsar da Inuwa Yahaya a matsayin gwamna
An tsaurara matakan tsaro a Gombe yayinda aka rantsar da Inuwa Yahaya a matsayin gwamna
Asali: UGC

Magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun kasance suna rawa da murna a ciki da wajen filin wasan mai iya daukan mutane 12,000.

KU KARANTA KUMA: Allah kadai zai iya kare iyakokin Najeriya ba Yansanda ba – Shugabannin tsaro

Shuwagabannin gargajiya da na addinai sun halarci bikin har da sarkin Gombe, Alh. Abubabar Shehu-Abubakar III.

An rantsar da Yahaya wanda aka haifa a ranar 9 ga watan Oktoba, 1969 a yankin Jekafari, jihar Gombe, a matsayin gwamna na hudu a jihar bayan marigayi Abubakar Hashidu, Sanata Danjuma Goje da gwamnan da ya gabata, Ibrahim Dankwambo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel