Karshen alewa kasa: Aradu ta dira akan wani shahararren boka, ta halakashi

Karshen alewa kasa: Aradu ta dira akan wani shahararren boka, ta halakashi

Tsawa da tartsatsi sun kashe wani sanannen boka a garin Aramoko dake cikin karamar hukumar Ekiti ta yamma a jahar Ekiti, mai suna Babatunde Sule, a ranar Talata, 28 ga watan Mayu, ini rahoton jaridar Leadership.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na rama yayin da boka Sule ke zaune a cikin dakinsa dake unguwar Oke-Oja, jim kadan bayan tsayawar ruwan sama da aka sha kamar da bakin kwarya.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta yi caraf da kanin sakataren gwamnatin Zamfara dauke da naira miliyan 60

Karshen alewa kasa: Aradu ta dira akan wani shahararren boka, ta halakashi

Karshen alewa kasa: Aradu ta dira akan wani shahararren boka, ta halakashi
Source: Twitter

Bayaga aikin bokanci da bin addinin gargajiya, boka sule ma’aikaci ne a majalisar dokokin jahar Ekiti, haka zalika shine shugaban mabiya addinin gargajiya na yankin, sai dai abinka da ajali, sai gashi kwarankwatsa ta rutsa dashi.

Wani makwabcin boka Sule daya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ruwan da aka yi yazo da da tsawa sosai, wanda hakan ya tsorata jama’a kowa ya kulle kofofi da tagogin dakinsa, tsayawan ruwan keda wuya sai boka sule ya fara girkin abinci, yana cikin girkin ne tsawa ta saukan masa a kirji, nan takeya fadi matacce.

Makwabcin yace shi ya fara ganin gawar boka sule kwance malemale cikin jini a dakin girki, daga nan sun yi kokarin sanar da mabiyansa yan addinin gargajiya ko akwai abinda zasu ya yi akai, amma ina, aikin gama ya gama.

Daga karshe yace sun fara gudanar da al’adar binne boka sule, kuma zasu kwashe kwanaki bakwai ana bukukuwa da shagulgulan binneshi. Sai dai kaakakin Yansandan jahar Ekiti, Cale Ikechukwu yace basu samu rahoton aukuwar lamarin ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel