CCB: Buhari da Osinbajo za su maida fam din da ke dauke da adadin dukiyarsu

CCB: Buhari da Osinbajo za su maida fam din da ke dauke da adadin dukiyarsu

Hukumar CCB mai binciken kadarorin ma’ikatan Najeriya ta bayyana Ranar da duk manyan jami’an gwamnati su maida fam din da su ka karba da ke nuna adadin dukiya da kadarorin da aka mallaka.

A yau Ranar Talata ne ake sa rai cewa ma’aikatan gwamnati za su maida takardun na CCB da su ka cike domin bibiyan samun su ganin cewa Ranar da za a kafa sabon gwamnati a Najeriya ya karaso.

Mun samu wannan labari ne bayan wani jawabi da hukumar CCB ta fitar a Ranar Litinin, 27 ga Watan Mayu a hedikwatar hukumar da ke babban birnin tarayya Abuja a lokacin da ake shirin kafa gwamnati.

Haka zalika ‘yan majalisar tarayya za su cike takardun na su, su maida ne kafin Ranar 8 ga Watan Yunin gobe. An nada wadannan ‘yan majalisa ne shekaru hudu da su ka wuce a Ranar 9 Watan Yuni.

KU KARANTA: Za a samu matsala tsakanin wasu Gwamnoni da za su sauka da Magadan su

CCB: Buhari da Osinbajo za su maida fam din da ke dauke da adadin dukiyarsu
Buhari da Osinbajo za su fadwa CCT adadin dukiyarsu
Asali: Twitter

Sauran wadanda hukumar CCB ta ke sa wa idanu sun hada da gwamnoni da mataimakansu, da shugabannin majalisar dattawa da na wakilai da kuma duk wasu /yan majalisar dokokin jiha da za su bar ofis.

Duk wanda zai hau kan kujera, zai bayyanawa hukumar CCB na kasar irin dukiyar da ya mallaka, haka kuma bayan ya bar ofis zai sake cike wani fam din ya bayyana duk kadarori da sauran arzikinsa.

Gwamna Rochas Okorocha na Imo ya bayyana cewa zai lissafawa hukuma jerin kadarorin na sa, haka zalilka gwamnan Bauchi mai shirin barin-mulki, Mohammed Abubakar, yayi irin wannan alkawari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel