Za ai hira ta musamman da shugaba Buhari a daren yau

Za ai hira ta musamman da shugaba Buhari a daren yau

A wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasa da ranar nan, ta bayyana cewar za a gudanar da wata tattaunawa ta musamman da shugaban kasa Muhammudu Buhari a gidan tslabijin na kasa (NTA).

Hirar da zata kasance ta kai tsaye a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu, zata zo da misalin karfe 10:00 na dare a gidan Talabijin na NTA da sauran kafafen yada labarai.

Da yake kara yada batun hirar da za ai da a yi da Buhari, kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya bukaci 'yan Najeriya su kasance tare da akwatinan talabijin dinsu da sauran kafafen yada labarai domin sauararon tattaunawar.

Muhammadu Buhari

Buhari
Source: UGC

Kazalika ya bukaci sauran gidajen Talabijin da Radiyo masu zaman kansu su jona shirin kai tsaye domin bawa 'yan Najeriya damar gani tare da sauraron tattaunawar daga dukkan sassan da suke a fadin kasar nan.

DUBA WANNNAN: Shirin bayar da tallafi: Maryam Uwais ta mayar wa Aisha raddi

Wannan shine karo na biyu a cikin shekaru hudu da shugaba Buhari zai gabatar da tattaunawa kai tsaye domin gabatar da jawabi ga 'yan kasa tare da amsa tambaoyin 'yan jarida masu yin tambaya kai tsaye yayin gabatar da hirar.

A baya an sha yin kiraye-kiraye a kan shugaba Buhari ya gudanar da hira irin wannan domin yiwa 'yan Najeriya jawabi a kan halin da kasa ke ciki, musamman ta fuskar tabarbarewar tsaro a wasu sassa na kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel