A karon farko, Kogunan Gusau ya yi magana kan ibtila'in rasa kujerarsa

A karon farko, Kogunan Gusau ya yi magana kan ibtila'in rasa kujerarsa

Dan takarar kujera gwamnan jihar Zamfara karkashin jam'iyyar All Progressive Congress APC kuma wanda ya lashe zaben, Mukhtar Shehu, ya yi magana karo na farko bayan kwace kujerarsa da kotun koli tayi ranan Juma'a, 24 ga watan Mayu, 2019.

Muktar Shehu ya lashe zaben gwamnan jihar Zamfara da aka gudanar a ranar 23 ga watan Mayu. 2019.

Amma sakamako rashin gudanar da zaben fidda gwani da jam'iyyar All Progressive Congress APC tayi, babban kotun Najeriya;kotun koli ta yi fatali da dukkan kuri'un aka kadawa APC a zaben bana.

KU KARANTA: Buhari zai garzaya jihar Gombe yau

A jawabinsa, Muktar Shehu yace: "Lallai mulki da girma ya tabbata ga Allah kuma shi ke baiwa duk wanda ya ga dama mulki."

"Ya ku yan'wana maza da mata a jam'iyyar APC, ina son yin amfani da wannan dama wajen mika godiyata gareku kan goyon baya da soyayyan da kuka nuna mana a wannan lokacin zaben."

"Jam'iyyarmu ta lashe zabe amma doka ta kwace. Wannan abin takaici ne ga jam'iyyarmu a jihar Zamfara, amma ibtila'i ne ga hadin kanmu."

"Ina rokon Allah ya baiwa gwamnatin da ke shigowa ikon kawo karshen matsalar tsaro da jihar ke fama da shi kuma ina addu'an cewa wannan nasara da suka samu, zai kawo cigaba garemu da rana gobenmuu gaba daya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel