Kadan daga cikin tarihin Bello Matawalle, sabon gwamnan Zamfara

Kadan daga cikin tarihin Bello Matawalle, sabon gwamnan Zamfara

-Yayin da ya rage kasa da mako guda kan a rantsar da sabbin gwamnonin jihohi, Zamfara ta samu sabon gwamna daga jam'iyar PDP.

Sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kasance cikin siyasa a matakin jiha da ma kasa baki daya na tsawon lokaci.

Mai shekaru 49 a duniya, zababben gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam’iyar PDP ya kasance cikin siyasa tsawon shekaru 20 kenan yanzu, inda ya taba rike mukamin kwamishina da kuma dan majalisar wakilai ta tarayya.

Zakaran da Allah Ya nufa da cara: Bello Matawalle zai kasance gwamnan Zamfara duk da ya fadi zabe
Bello Matawalle
Asali: Twitter

KU KARANTA:Tsuntsu daga sama gasasshe: Bello Mutawwalle na PDP zai zama gwamna a Zamfara

Zaben 9 ga watan Mayun 2019 shi ne karonsa na farko da ya tsaya takarar gwamna, amma bai yi nasara ba kasancewar hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta baiwa jam’iyar APC damar tsaida yan takararta bai wuce awa 24 ayi zabe ba.

Hukumar zaben mai zaman kanta ta bayyana dan takarar APC Muktar Idris a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben.

Farfesa Kabiru Bala na jami’ar Ahmadu Bello Zaria shi ne ya bada sanarwar zaben kamar haka, jam’iyar APC ta samu kuri’a 534,541 yayinda Matawallen PDP ya sha kasa da kuri’a 189,452.

Matawalle sam bai aminta da wannan sakamako ba, inda yayi ikirarin cewa “sai ya kwaci hakkinsa” a kotun sauraren korafe-korafen zabe.

Yace nasararsa ce aka baiwa APC kuma akwai kananan hukumomin da aka samu tangarda saboda magudin zabe da jam’iyar ta APC ta yi.

A hankali ya cigaba da bin karar tun daga kotun sauraren korefe-korefen zabe har zuwa kotun koli, wacce ta damka mashi nasara a ranar Juma’a inda ta ce duk kuri’un APC “ asarar kuri’a ne”.

An haifi Bello Matawalle a ranar 12 ga watan Disamba, 1969 a karamar hukumar Maradun. Ya kuma yi karatun firamare a makarantar Maradun Township Primary School wacce ya kammala a 1979. Ya kuma yi karatu a Kwalejin fasaha da kere-kere ta Yaba dake Legas da kuma jami’ar Thames Valley dake Landan.

Yayi kwamishinan lafiya tun lokacin tsohuwar jihar Sokoto, ya kuma koyar a makarantar sakandiren mata ta Moriki da Kwatarkwashi. Daga nan sai ya samu aiki a ma'aikatar ruwa ta kasa inda ya shiga siyasa a shekarar 1998 karkashin jam'iyar UNCP.

Daga shekarar 1999 zuwa yanzu Bello Matawalle ya kasance dan siyasa wanda ya sauya jam'iya alokuta da dama kuma rike mukaman a gwamnati, ciki akwai kwamishina da kuma dan majalisa mai wakiltar Bakura da Maradun a majalisar dokokin tarayya wanda yayi na tsawon shekara takwas daga 2003 zuwa 2011.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel