Ikon Allah: Angulun da muka tsare ta ci N30,000 cikin kwanaki shida - Hukumar Yan sanda

Ikon Allah: Angulun da muka tsare ta ci N30,000 cikin kwanaki shida - Hukumar Yan sanda

Hukumar yan sandan jihar Adamawa ta bayyana cewa Ungulun da ta tsare a garin Mahia dake jihar Adamawa ta ci naman N30,000 cikin kwanaki shida a ofishin hukumar.

Jami'an yan sanda sun damke Angulun ne tare da wata mata bayan al'umman garin sun koka cewa dabbar na basu tsoro.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Othman Abubakar, ya ce hukumar za ta kashe makudan kudi muddin ta cigaba da tsare wannan tsuntsu.

Ya bayyana cewa har yanzu hukumar na cigaba da bincike kan bayyanar wannan Angulu.

KU KARANTA: Hukuncin kotun koli: Jerin sunayen zababbun yan jam'iyyar APC na jihar Zamfara da sukayi asarar kujerunsu

Kwamishanan yan sandan jihar, Adamu Audu Madaki, ya bayyanawa manema labarai cewa an damke dabbar da matar ne bayan karar da wani babba a garin ya shigar hukumar saboda tsoron da Angulun ke basu da kuma tunanin cewa da walhakin wani sabon shirin kawo hari ne garin.

Ya kara da cewa kwanakin baya da wata mata ta kawo Ungulu guda uku garin Mahia, yan Boko haram sun kawo harin garin.

Tun lokacin da labarin wannan Ungulu ya yadu, wasu jama'an gari suka fara yada jita-jitan cewa ai wata mata ce da akame garkame a ofishin yan sanda ta rikide ta zama Angulu.

Maiha na daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da kungiyar Boko Haram ya kwace tsakanin 2014 da 2015 kafin Soji suka kwato garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel