Muhimman ayyukan ibada 10 da ya kamata mai azumi yayi a goman karshe na Ramadana

Muhimman ayyukan ibada 10 da ya kamata mai azumi yayi a goman karshe na Ramadana

A daidai lokacin da azumin watan Ramadana ke kara ja, a yanzu haka ana gab da shiga goman karshe na wannan wata mai tarin falala.

Dararen goman karshe na wannan wata sune mafi darajar darare ga Dan Adam, ayyukan Alkhairi a cikin su na da matukar girman daraja fiye da sauran dararen da suka gabata.

Goman karshe na farawa ne daga shan ruwa na rarar da azumi ya cika ashirin dai-dai har zuwa ganin watan Sallah.

Goman karshe suna da matukan falala, Annabi yana son su, kuma yana raya su da ibada. Idan goman karshe suka zo, Annabi (SAW) yana kara jajircewa wajen yin ibada, yana raya dararen sannan kuma ya nisanci matansa.

Muhimman ayyukan ibada 10 da ya kamata mai azumi yayi a goman karshe na Ramadana
Muhimman ayyukan ibada 10 da ya kamata mai azumi yayi a goman karshe na Ramadana
Asali: UGC

Ga wasu daga cikin ayyuka masu tarin falala da ya kamata Musulmi kuma mai azumi ya jajirce wajen aikata su domin samun dacewa:

1. Ittikafi: A nan Musulmi kan yi kaura zuwa masallaci domin ya samu ikon shagaltuwa da ibada. Hadisi ya ingata daga Imamul Bukhari da Muslim, cewa Annabi (SAW) ya lizimci Ittikafi duk goman karshe har ya bar duniya.

2. Karatun Al-Kur’ani: Yana daga cikin manyan ibadu a goman karshe, musulmi ya mayar da hankali a karatun Al-Kur’ani mai girma, cikin tunani da khushu’i da bibiyan ma’anarsa, Mala’ika Jibirilu yana bibiyan Al-Kur’ani tare da Annabi (SAW) a cikin watan Ramadana.

3. Neman daren Lailatul Kadari: Duk Musulmin da ya dace da wannan dare cikin ibada da takawa, da ikhlasi, to ibadarsa na wannan dare kadai, tafi alkhairi da ibadar da zai yi a cikin rayuwarsa gaba dayanta.

4. Yawaita zikiri da ambaton Allah na da matukar falala a wadannan darare.

5. Kyautata halaye na kwarai da tausayi.

6. Kauracewa dukkanin ayyukan sabo da zunubi, domin girmansu yafi tsanani a wannan lokaci.

7. Tsayuwar dare (Kiyamul Laili): Annabin tsira ya kasanci yana raya wadannan darare da ibada kuma yana tada iyalansa domin su yi ibada.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 17 da Buhari ya fada ma yan majalisarsa masu barin gado

8. Yawaita Ciyarwa da Sadaka da kyauta: Mazon Allah (SAW) ya kasance kyautarsa ta fi yawa a cikin Ramadana.

9. Kaucewa zalunci da kuntatawa mutane ko cutar dasu.

10. Jajircewa da Addu’ah: yawaita addu’o’i, ga kai, iyaye, iyalai da kasa. Yawaita neman gafara, da rangwame da dukkan bukatun duniya da

lahira. Neman tsari daga wuta da rokon dacewa Al-Jannah.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel