Furuci kan Boko Haram: Gigin tsufa na damun Obasanjo – Dan majalisa Magaji

Furuci kan Boko Haram: Gigin tsufa na damun Obasanjo – Dan majalisa Magaji

Wani dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Magaji Da’u Aliyu, ya bayyana cewa abun kunya ne ace tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo na iya sauya yadda lamarin tsaro yake a kasar saboda makirci.

Magaji ya bayyana cewa ga dukkan alamu gigin tsufa na damun tsohon Shugaban kasar, shiyasa har ya furta zancen.

“Abun kunya ne ace irin wannan furuci na fitowa daga Obasanjo. Ya kasance Shugaban kasa a mulkin soja da na farin hula a kasar nan. Yana da bayanai da dama. Ina ganin dai tsufa na damun shi. Idan ba tsufa ba, bana tunanin ya kamata ya fadi irin wannan furucin. Idan ka duba lamarin, wadanda ayyukan ta’addanci ya cika dasu Musulmai ne, Fulani ma. Kafin ka ji ance an kashe wani, an kashe Musulmai da dama.

Furuci kan Boko Haram: Gigin tsufa na damun Obasanjo – Dan majalisa Magaji
Furuci kan Boko Haram: Gigin tsufa na damun Obasanjo – Dan majalisa Magaji
Asali: UGC

“Muna rokon Allah ya kawo mana karshen wannan abu. Amma kada ya bari banbancin akidar siyasarsa da Shugaban kasa ya sanya shi yin kowani irin furuci,” inji shi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta ce kalaman da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kan yakin da gwamnati keyi da Boko Haram da ISWAP na iya janyo rabuwar kai tsakanin mabiya addinai da mabanbanta kabila a Najeriya.

Gwamnatin ta kuma ce kalaman na da matukar muni kuma abin kunye ne a rika samun dattajo kamar tsohon shugaban kasar yana furta irin wannan kalaman.

KU KARANTA KUMA: Masu zanga-zanga sun dauki gawawwaki 18 zuwa gidan gwamnati da fadar sarki

A sanarwar da ministan yadda labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar ranar Talata a Abuja, ya ce abin takaici ne mutumin da ya yi yaki domin tabbatar da hadin kan Najeriya ya kuma juya yana neman raba kan kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel