Jihohi da yawa za su talauce idan aka fara biyan sabon albashi - Tsohon Kwamishinan Kudi
- A hasashen da wani tsohon kwamishinan kudi na jihar Legas ya bayar ya bayyana cewa jihohi da yawa za su talauce a kasar nan da zarar an fara biyan sabon albashi
- Ya bayyana cewa koda an fara biyan sabon albashin, albashin ba zai yi wani tasiri ga al'umma ba saboda yadda darajar naira ta fadi a kasuwannin duniya
Tsohon kwamishinan kudi na jihar Legas, Dr. Adebayo Adewusi, ya ce jihohi da yawa za su talauce sanadiyyar karin albashin da aka yi na naira 30,000.
Ya ce wasu jihohin basu da arzikin da za su iya biyan ma'aikatan su sabon albashin, kuma abubuwa za su iya rincabewa idan aka yi watsi da karbar kudin shiga.
Adewusi, tsohon shugaban WEMABOD, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a wata hira da suka yi ranar Litinin.
Bayan haka kuma ya yi bayani game da karin albashin 18,000 da aka yi a shekarar 2015, Adewusi ya ce sabon albashin bai da tasiri, idan aka yi la'akari da irin matsalar tattalin arzikin da ake fama dashi, da kuma yadda naira ta fadi a kasuwannin duniya.
Ya kara da cewa a 2015 kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki, albashin 18,000 daidai yake da dalar Amurka 122, amma yanzu sabon albashin 30,000 daidai yake da dalar Amurka 85, saboda darajar naira ta fadi sosai a kasuwannin duniya.
KU KARANTA: Wike ya yi alkawarin bani cin hancin biliyoyin naira idan na taya shi magudin zabe - Janar Jamil Sarham
"Saboda haka idan kuka yi la'akari da magana ta, sabon albashin ma ba wai zai ishi mutane bane, amma maganar gaskiya a nan ita ce sabon albashin da ake ta faman magana akan shi jihohi da yawa ba za su iya biya ba, saboda basu da arzikin biyan wannan kudaden a wannan lokacin."
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta na bukatar ta kara kudin shiga na jihohi domin samun damar biyan wannan kudin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana
Asali: Legit.ng