Yanzu-yanzu: An damke yan baranda 15 da suka addabi jihar Sokoto (Hotuna)

Yanzu-yanzu: An damke yan baranda 15 da suka addabi jihar Sokoto (Hotuna)

Jami'an rundunar atisayen Operation Puff Adder na hukumar yan sanda sun damke wasu ya taki zama 15 a karamar hukumar Isa dake jihar Sokoto, arewa maso yammacin Najeriya.

Yayin bayyana yan barandan a hedkwatan hukumar dake cikin garin Sokoto, kwamishanan yan sandan jihar, Ibrahim Kaoje, yace an damke wadannan yan barandan ne a karshen makon da ya gabata yayin sintiri.

Yanzu-yanzu: An damke yan baranda 15 da suka addabi jihar Sokoto (Hotuna)
An damke yan baranda 15
Asali: Facebook

Mista Ibrahim ya kara da cewa yan barandan na daga cikin yan bindigan suke guduwa daga jihar Zamfara sakamakon matsin lamba da wutan da rundunar sojoji ke musu a jihar.

Daga cikin abubuwan da aka samu a hannunsu sune bindigogi, adduna, babura, guru da layu da sauransu.

Ya yi kira ga al'ummar gari sun baiwa jami'an tsaro goyon baya ta hanyar cinne wanda zai taimaka wajen kawo karshen yan barandan da suk tada zaune tsaye a birnin Shehu.

Yanzu-yanzu: An damke yan baranda 15 da suka addabi jihar Sokoto (Hotuna)
Yanzu-yanzu: An damke yan baranda 15 da suka addabi jihar Sokoto (Hotuna)
Asali: Facebook

A labari mai kama da haka, Hukumar yan sandan Najeriya ta samu nasarar damke wasu masu garkuwa da mutane 13 da suka addabi jihar Katsina wanda ya kai ga sace surukar gwamnan jihar, Aminu Bello Masari a ranar 8 ga watan Fabrairu, 2019.

Kwamishanan yan sandan jihar Katsina, ya bayyanasu ga manema labarai a yau Litinin, 20 ga watan Mayu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel