Dalibi ya kashe kansa saboda ya fadi jarabawa

Dalibi ya kashe kansa saboda ya fadi jarabawa

Zakah Timi Ebiweni, dalibi dan aji 3 a tsangayar koyar aikin likita na Jami'ar Niger Delta, (NDU) na jihar Bayelsa ya kashe kansa.

Rahotanni sun ce Ebiweni da dauki rayuwarsa ne ta hanyar tsunduma kansa cikin wani rafi da ke kusa da jami'ar a Amassoma da ke kudancin garin Ijaw sakamakon fadi jarabawa da ya yi.

Kimanin dalibai 50 cikin 169 da suka rubuta jarabawar na koyar aikin likitanci sun fadi jarabawar kamar yadda Sahara Reporters ta wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Asinim Butswat ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce ba a shigar da rahoto a ofishin 'yan sanda ba.

Dalibi ya kashe kansa saboda ya fadi jarabawa

Dalibi ya kashe kansa saboda ya fadi jarabawa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

Mai magana da yawun jami'ar, Ndoni Ingezi tayi magana da majiyar Legit.ng inda ta ce: "Eniweni ya kashe kansa ne bayan ya samu labarin cewa yana daya daga cikin dalibai 22 da za a kora daga jami'ar saboda sun fadi jarabawa.

"Kamar yadda aka saba dole kowane dalibi ya rubuta jarabawa MBBS ya yi nasara kafin ya tafi mataki na gaba a karatunsa.

"Amma Ebiweni da wasu dalibai 21 sun fadi jarabawar kuma ba su ci makin da ya dace a bari su sake maimaita shekarar ba saboda haka za a kore su daga tsangayar.

"Kamar yadda ka'idar ya ke, ba a fadawa dalibai za a sallame su ba tare da an hada su da kwararru da za su basu shawarwari ba.

"A lokacin da aka fadawa Ebiweni cewar za a kore shi daga tsagayar, ya amince da kaddara kuma ya yi tafiyarsa.

"Amma daya baya kawai sai muka ji labarin cewa matashin ya kashe kansa.

"An ciro gawarsa daga rafin an ajiye a dakin ajiyar gawarwaki na Sabageria."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel