Mutane 2 sun sheka barzahu bayan gamuwa da ajalinsu a cikin ruwan Kano

Mutane 2 sun sheka barzahu bayan gamuwa da ajalinsu a cikin ruwan Kano

Wani dan matashin yaro mai suna Umar Murtala ya gamu da ajalinsa a cikin wani kandamin ruwa dake cikin garin Kano, a unguwar Gwazaye gab da cibiyar matasa ta Sani Abacha dake cikin karamar hukumar Gwale.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar kwana kwana ta jahar Kano ce ta bayyana haka ta bakin kaakakinta, Alhaji Saidu Mohammed a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, inda yace lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayu da misalin karfe 5 na yamma.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Durbin Katsina, hakimin Jikamshi yayi murabus daga mukaminsa

“Da misalin karfe 5 na yamma muka samu kira cikin gaggawa daga wani mutumi mai suna Abubakar Aliyu, inda yace sun hangi gawar wani matashi mai suna Murtala tana yawo a saman ruwan wani Kandami.

“Ba tare da bata lokaci ba muka aika da jami’anmu zuwa unguwar da lamarin ya faru, inda suka isa da misalin karfe 5:15 na yamma, nan da nan muka ciro gawarsa daga cikin ruwan, muka mikata ga mahaifinsa, Muratala Salisu, sai dai har yanzu muna gudanar da bincike kan musabbabin lamarin.” Inji shi.

Haka zalika a wani labarin makamancin wannan, Alhaji Saidu yace wani dan saurayi, Mohammed Shaharali ya gamu da ajalinsa yayin da ya fada cikin wani tafkin ruwa wanda hakan yayi sanadiyyar nutsewarsa.

Kaakakin yace wannna lamari kuma ya faru ne da safiyar Lahadi, 19 ga watan Mayu a unguwar Ladanai cikin karamar hukumar Nassarawa ta jahar Kano, a cewar Kaakakin sun samu nasarar ceto Muhammed da ransa, amma daga bisani yace ga garinku nan a Asibiti.

Daga karshe kaakakin ya gargadi jama’a game da wanka a cikin ruwan tafki, kwami da kandami saboda bincike ya nuna an samu karuwar mace macen mutane a cikin ruwa a jahar Kano tun bayan shigowar yanayin zafi a jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumin Ramadan sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel