Za’a sha ruwa kamar da bakin kwarya a jahohin Arewa guda 4 a yau – Gwamnati

Za’a sha ruwa kamar da bakin kwarya a jahohin Arewa guda 4 a yau – Gwamnati

Hukumar gwamnatin tarayya dake aikin kula da yanayin sararin samaniya, NiMet ta sanar da cewa za’a samu tattaruwar hadari da yiwuwar samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu a sassan yankunan kasar a yau Litinin, 20 ga watan Mayu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito NiMet ta bayyana haka ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayu cikin wata sanarwa data fitar a babban birnin tarayya Abuja, inda tace za’a samu taruwar hadari da yiwuwar ruwan sama mai karfi a jahohin Kaduna, Jos, Neja da Kwara da safiyar yau.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai hari cocin Kaduna, sun yi garkuwa da Fasto da yan mata 10

Haka zalika hukumar ta hakaito akwai yiwuwar samun tsawa da ruwan sama kamar da bakin kwarya a jahohin Filato, Abuja, Taraba, Nassarawa, Adamawa da Benuwe, sa’annan yanayin jahohin zai kai digiri 12 zuwa 25 a ma’aunin celcius da daddare.

Bugu da kari sanarwar tace har ila yau akwai wasu jahohin Arewa da zasu iya samun tsawa amma ba tare da samun ruwan sama mai karfi ba, jahohin kuwa sune Kebbi, Sakkwato, Bauchi da Gombe, yayin da yanayin jahohin zai yi kasa tsakanin 24 zuwa 28 a ma’aunin Celcius a daren yau.

Daga karshe sanarwar hukumar NiMet ta bayyana cewa za’a samu matsakaicin ruwan sama a jahohin kudu masu yammacin kasarnan, tare da samun digiri 31 zuwa 34 na yanayi da rana, yayin da yanayin dare zai sauka tsakanin digiri 22 zuwa 24 a ma’aunin Celcius.

“Akwai alamu masu karfi dake nuna cewa za’a samu yanayi mai kyau a Najeriya cikin sa’o’I 24 masu zuwa.” Inji NiMet.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel