Mutane 6 da suka fi kowa girman hannun jari a kamfanin sadarwa na MTN

Mutane 6 da suka fi kowa girman hannun jari a kamfanin sadarwa na MTN

A yayin da ya kasance mafi girman kamfanin sadarwa a nahiyyar Afirka ta fuskar masu amfani da kuma girman kasuwanci, kamfanin MTN a makon da ya gabata ya fidda jerin sunayen mutane masu rike da babban kaso na hannun jari.

Kamar yadda da hukumar kuka da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC ta fitar a karshen shekarar da ta gabata, akwai fiye da 'yan Najeriya miliya sittin da bakwai da ke amfani da layin sadarwa na kamfanin MTN.

Kamfanin sadarwa na MTN
Kamfanin sadarwa na MTN
Asali: UGC

A yayin da ya kasance a mataki na biyu ta fuskar daraja a dukkanin harkokin kasuwanci na Najeriya, mujallar fidda kididdiga ta duniya Forbes, ta ce kamfanin sadarwar na MTN na da daraja ta kimanin dalar Amurka biliyan shida yayin da kamfanin Siminti na Dangote da ya ke a mataki na farko ke da daraja ta kimanin Dalar Amurka biliyan 8.3.

Ga jerin sunayen Mutane shida dake kan sahu na gaba masu mallakin mafi girman hannayen jari a kamfanin sadarwa na MTN:

1. Victor Odili

Victor Odili shi ne mai mallakin mafi girman kaso na hannayen jari a kamfanin sadarwa na MTN. Yana da hannayen jari kimanin 806,886,900 wanda darajar su ta kai kimanin Dalar Amurka miliyan 244 (Naira biliyan 87.7).

2. Pascal Dozie

Pascal Dozie yana da hannayen jari kimanin 340,409,900. Darajar hannayen jari da Pascal ya mallaka a kamfanin sadarwa na MTN ta kai kimanin Dalar Amurka miliyan 102 (Naira Biliyan 37.07).

3. Sani Muhammad Bello

Mai kamfanin man fetur na Amni International, Sani Muhammad Bello, yana da hannayen jari 265,092,150 a kamfanin sadarwa na MTN wanda darajar su ta kai kimanin Dalar Amurka miliyan 80.1 (Naira Biliyan 28.87).

4. Babatunde Folawiyo

Tunde Folawiyo yana da mallakin hannayen jari 218,815,100 kaso 1.07 cikin dari a kamfanin sadarwa na MTN wanda darajar su ta kai kimanin Dalar Amurka miliyan 66.1 (Naira Biliyan 23.83).

5. Gbenga Oyebode

A yayin da Gbenga Oyebode ke da kaso 0.89 cikin dari na hannun jari a kamfanin sadarwa na MTN. Gbenga na da mallakn hannayen jari 181,776,250 wanda darajar su ta kai kimanin Dalar Amurka miliyan 55 (Naira Biliyan 19.8).

6. Ahmed Dasuki

Shugaban kamfani hako ma'adanan kasa na Drill Masters Africa da ke kasar Ghana, Ahmed Dasuki, yana da hannayen jari 152,717,850 a kamfanin sadarwa na MTN wanda da darajar su ta kai kimanin Dalar Amurka miliyan 53.75 (Naira Biliyan 19.35).

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel