Tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida na nan da ransa bai mutu ba - Maiyoyi

Tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida na nan da ransa bai mutu ba - Maiyoyi

- Majiyoyi sun karyata labarin mutuwar tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida

- Wata jaridar yanar gizo ta wallafa a ranar Juma’a cewa tsohon shugaban kasar ya mutu, a ranar Juma’a, 17 ga wata Mayu

- Amma an tattaro cewa Babangida tare da yaransa, makusantan abokansa da hadimansa sunyi bude baki tare a gidansa da ke Hill top a ranar Juma’a, 17 ga watan Mayu

Sabanin rade-radin da ke yawo cewa tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya mutu, an tabbatar da cewar yana nan da ransa cikin koshin lafiya.

Wata jaridar yanar gizo ta wallafa a ranar Juma’a cewa tsohon shugaban kasar ya mutu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Janar Babangida na nan da ransa kuma yana harkokin rayuwarsa.

Tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida na nan da ransa bai mutu ba - Maiyoyi

Tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida na nan da ransa bai mutu ba - Maiyoyi
Source: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa Babangida tare da yaransa, makusantan abokansa da hadimansa sunyi bude baki tare a gidansa da ke Hill top a ranar Juma’a, 17 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Tsugune bata kare ba: Gwamnatin jihar Kano za ta canjawa sarkin Kano masarauta

"Bama haka ba Babangida ya saba shan ruwa da mutane daban-daban kuma hakan ne ke gudana tunda aka fara azumin wannan shekarar, Matacce baya iya azumi hakan na nuna maku cewa IBB na raye,” cewar majiyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel