Ragowar kudin Paris Club: Za a yi wa jihohi rabon N649bn

Ragowar kudin Paris Club: Za a yi wa jihohi rabon N649bn

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kwanan nan za ta raba ma gwamnatocin jihohi naira biliyan 649.434 ragowar kudin Paris Club da yayi saura.

Ministar kudi, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, a ja ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu, lokacin da ta ke jawabi ga manema labarai, a taron ‘yan jaridu da ta shirya.

Wannan adadi dai bai kai ma naira bilyan 694.560 da Babban Bankin Najeriya (CBN ) ya biya cikin watan Maris, 2019 ba.

Aan tattaro cewa bambancin canjin musayar kudade ne ya kawo wannan gibi na sama da naira milyan 40.

Ministaar ta ce nan ba da jimawa ba za a fara raba wa jihohi kudaden, a matsayin kashin karshe na kudaden Paris Club da aka sha ba su a baya.

Ragowar kudin Paris Club: Za a yi wa jihohi rabon N649bn

Ragowar kudin Paris Club: Za a yi wa jihohi rabon N649bn
Source: Facebook

Zainab ta ce wannan tsari na bai wa jihohi kudaden Paris Club, ya samu nasara gagarima wajen cicciba kasar nan ta fita daga matsin tattalin arziki da ta yi fama da shi.

KU KARANTA KUMA: Babban bankin Najeriya na shirin farfado da masaku 50 cikin shekaru 4

An gudanar da tsarin ne a karkashin Shirin Farfado da Tattalin Arziki a karkashin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Zainab ta kara da cewa sakamakon nasarar wannan shiri, a yanzu Najeriya na kan hanyar dorewa a kan ingantaccen tattalin arziki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel