Abubuwa 10 da mai fama da gyambon ciki zai kiyaye a lokacin Azumi

Abubuwa 10 da mai fama da gyambon ciki zai kiyaye a lokacin Azumi

Wani shahararren masani a harkar lafiya ya yi arin haske akan yadda mai fama da matsalar gyambon ciki wato Ulsa zai gudana da azumin Ramadana cikin sassauci, hakan zai samu ne idan har ya nisanta kansa daga cima da ka iya tado ciwon.

Ana gane alamu wannan cuta ne ta hanyoyi da sukahada da amai, ciwon ciki, ciwon kirji,sanan cikin mutum bai iya markada aminci yada ya kamata da sauran su.

Abubuwa 10 da mai fama da gyambon ciki zai kiyaye a lokacin Azumi

Abubuwa 10 da mai fama da gyambon ciki zai kiyaye a lokacin Azumi
Source: UGC

Hanyoyin guje wa tada cutar a lokacin Ramadan sun hada da:

1. Mutum yayi gaggawan cin dabino da zaran an sha ruwa, haakan na taimakawa wa mai dauke da cutar.

2. A guji cin abincin da aka soya ko kuma abincin dake da mai dayawa.

3. A kaurace ma shan abubuwa masu tsami kamar su kunun tsamiya, kunun zaki, koko, lemu, lemun tsami da sauran su.

4. Ana iya shan madaran da aka dama da ruwan sanyi ko kuma da ruwan zafi a lokacin da za a yi sahur domin hana cutar tasowa.

5. Shan ruwa kwakwa ma na taimakawa sosai.

6. Sanya ganyayyaki a abinci, kamar su kabeji, Latas da sauransu ma na taimakawa.

7. Kamata ya yi mai dauke da wannan cuta ya ci abinci kadan-kadan bayan an sharuwa.

KU KARANT KUMA: Jami’an DSS sun gayyaci wani shahararren malamin addinin Musulunci, sun kuma tsare shi a Katsina

8. A karace ma cin abinci dake da yaji.

9. A kaurace ma cin abinci mai nauyi.

10. A tanaji maganin rage radadin Ulsa din a kusa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel