Hukumar Kwastam ta fitar da muhimmiyar sanarwa ga masu neman aiki

Hukumar Kwastam ta fitar da muhimmiyar sanarwa ga masu neman aiki

A cigaba da shirinta na daukar sabbin ma'aika fiye da dubu uku a fadin kasar nan, hukumar hana fasa kwauri da aka fi kira da 'Kwastam' ta fitar da sanarwar neman masu neman aiki da suka aike da takardun su, da suyi watsi da labarin dake yawo a kafafen sadar wa cewar za ta gudanar da jarrabawa.

Hukumar ta kwastam ta ce labarin ba gaskiya ba ne, a saboda haka masu neman aikin su kiyaye da kafafen dake yada labarin.

Sannan ta kara da cewa yanzu haka hukumar na matakin tantance takardu da bayanan masu sha'awar aiki da ita domin sanin adadin mutanen suka cancanta ta aike wa sakon gayyata zuwa rubuta jarraba wa.

A sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook, ta ce da zarar ta kammala tantance wadanda suka cancanta, za ta fitar da sunayen su, sannan za ta tuntube su a kan lambobin wayar su da kuma adireshin email.

Hukumar Kwastam ta fitar da muhimmiyar sanarwa ga masu neman aiki

Shugaban hukumar Kwastam: Hameed Ali
Source: Depositphotos

Kazalika, tayi kira ga masu neman aiki da su yi hankali da sakonnin da 'yan damfara ke aike wa da sunan hukumar kwastam ta kasa.

A wani labarin na Legit.ng mai alaka da wannan, kun ji cewar hukumar Kwastam ta kasa ta ce akalla mutane 524,315 suka samu nasarar kamalla cika aikin da suka bayyana cewa zasu dauki ma'aikata mutum 3,200.

DUBA WANNAN: Buratai ya yi banbami a kan mutuwar babban soja da wasu kananan sojoji a Borno

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Mista Joseph Attah shi ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya jiya Litinin a Abuja.

A ranar 17 ga watan Afrilu, ne hukumar kwastam ta bude shafinta na yanar gizo domin daukar ma'aikata mutum 3,200.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel