Yan fadan Saraki da Dogara sun fara ja da baya yayinda wa’adin shugabancinsu ya zo karshe

Yan fadan Saraki da Dogara sun fara ja da baya yayinda wa’adin shugabancinsu ya zo karshe

Kasa da kwanaki 30 kafin rantsar da majalisar dokoki na tara, yawan masu yiwa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara fadanci ya ragu sosai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa yawan yan majalisa da kan kewaye shugabannin biyu don nuna girmamawa a gare su ya ragu, sai dai hakan bai rasa nasaba da sauyin shugabanni da za a samu a watan Yuni.

Kafin yanzu, ya kan kwashi kimanin mintuna 15 zuwa 20 kafin shugabannin su samu shiga majalisa saboda yawan yan majalisa da sauran mutane da kan jeru domin su gaisa dasu sannan suyi musabaha.

A yan kwanakin nana bun ya sauya, yanzu yana daukarsu kasa da mintuna biyar daga Saraki har Dogara wajen shiga ofishin sun a majalisar saboda raguwan mutane masu gaishe dasu da masu masu girma.

Yan fadan Saraki da Dogara sun fara ja da baya yayinda wa’adin shugabancinsu ya zo karshe
Yan fadan Saraki da Dogara sun fara ja da baya yayinda wa’adin shugabancinsu ya zo karshe
Asali: Depositphotos

Majiyarmu ta bayyana cewa hatta ayyukan ofishinsu na raguwa sosai a yanzu duba ga raguwar yawan masu kawo ziyara da kuma na masu kira a waya.

Hatta ga ma’aikatan ofishinsu ma ayyuka ya ragu masu sosai na yawan zirga-zirga.

Wani babban dan majalisa na PDP a majalisar wakilai wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana lamarin a matsayin ba sabon abu ba, amma bai yi dogon jawabi kan ko Dogara zai dawo a matsayin kakakin majalisa ba a watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An nemi kotun zabe ta dakatar da rantsar da Buhari

Shugaban majalisar dattawa Saraki ba zai dawo majalisar dokokin kasar na tara ba bayan faduwa da yayi a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu, inda Yahaya Oloriegbe na APC ya yi nasara.

Koda dai Dogara ya lashe zabe a mazabarsa ta Bogoro/Das/Tafawa Balewa, dan majalisar bai nuna ra’ayinsa na son sake takarar kujerar kakakin majalisa ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel