Ta'addanci: Buhari zai biya kungiyar Miyetti Allah N100bn domin samar da wuraren kiwo

Ta'addanci: Buhari zai biya kungiyar Miyetti Allah N100bn domin samar da wuraren kiwo

Binciken jaridar Independent da aka wallafa a ranar Lahadi ya tabbatar da cewa, akwai gagarumar barazana ta yunwa da kuma karancin abinci da ke tunkaro kasar nan muddin gwamnati ba ta kawo karshen ta'addanci musamman a yankunan jihar Zamfara, Kaduna, Katsina da kuma na kwana kwanan nan mai yaduwa cikin jihohin Neja da Nasarawa.

Baya ga wannan barazana, rahotanni sun bayyana cewa kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram tare da hadin kungiyar ta'adda ta yankin nahiyyar Afirka ta Yamma ISWAP, na ci gaba da samun mabiya daga kasashen Senagal, Sudan, Nijar da kuma sauran kasashen dake makotaka da Najeriya a yankin na nahiyyar Afirka.

Ministan harkokin cikin gida; Abdulrahman Dambazau

Ministan harkokin cikin gida; Abdulrahman Dambazau
Source: Depositphotos

Kamar yadda wani tsohon babban jami'in tsaro ya bayyana, fa'idantuwa da masaniyar hanyoyin kiwon dabbobi da suka ratsa cikin gonaki ya sanya masu zartar da ta'adanci musamman a yankunan Arewa maso Yamma ke ci gaba da cin karen su babu babbaka.

Tsohon jami'in dakarun sojin kasa na Najeriya ya fashin baki da cewa, harin da ya auku a makon da ya gabata ba tare da aune ba cikin yankin Ife-Ileshe na jihar Osun ya tabbatar yadda 'yan ta'adda suka karanci duk wani kwararo da sako na hanyoyi da wuraren kiwo da ke fadin kasar nan.

A ranar 5 ga watan Mayun da ta gabata, mashaida da dama sun bayyana yadda wata babbar mota mai dakon kaya dauke da 'yan ta'adda rike da bindigu suka datse matafiya a babbar hanyar garin Ikoyi da ke jihar Osun.

Yayin aukuwar wannan mummunar barazana, 'yan ta'adda sun yi garkuwa da babban Likita, Olayinka Adegbehingbe, na asibitin koyarwa da ke jami'a Obafemi Awolowa. Sun 'yanta shi bayan 'yan uwan sa sun biya makudan kudin fansa na Naira miliyan biyar.

Dangane da furucin sa akan wannan mummunar ta'ada ta garkuwa da mutane da ta zamto ruwan dare, gwaman jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya jaddada cewa akwai muhimmiyar bukata ta sake bayar da kofar tattaunawa da kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah.

Bayyanar wasu rahotanni a makon da ya gabata sun haskaka cewa, Ministan harkokin ci gada Abdulrahaman Dambazau, ya gana da jagororin kungiyar Miyetti Allah domin kulla shawarwari na kawo karshen kashe-kashe da zubar jinin da ake aukuwa a sanadiyar karancin wuraren kiwon dabbobi a kasar.

KARANTA KUMA: Huduba: Abubuwan da za a dage da su a lokacin Azumin Watan Ramadan

Domin samar da wadatattun wuraren kiwo, kungiyar ta makiyaya ta shigar da bukatar neman naira biliyan 160 domin tabbatuwar wannan kudiri. Sai dai gwamnatin shugaban kasa Buhari ta raja'a a kan fidda Naira biliyan 100 gwargwadon abin da ta misalta na ikon ta.

A yayin da gwamnatin tarayya da daura damarar fidda wannan dukiya, majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan kudiri ya yi daidai da shawarwari na gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, wajen samar da wadatattun wurare kiwo da kuma kawo karshen rikicin makiyaya da manoma.

Duba da kididdigar da ma'aikatar noma ta fitar a shekarar 2014, jihohin da za su ribaci dukiyar gwamnatin tarayya wajen samar da wuraren kiwo sun hadar da Borno, Adamawa, Filato, Jigawa, Katsina, Sakkwato, Benuwe, Kebbi, Kaduna, Kwara, Yobe, Kano, Bauchi, Taraba, Kuros Riba, Kogi, Neja, Enugu da kuma jihar Oyo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel